logo

HAUSA

Ma’aikatar lura da birnin Abuja za ta fara aikin rushe wasu rukunin gidaje da aka gina ba tare da izini ba

2023-03-14 09:53:57 CMG Hausa

A ranar Litinin 13 ga wata, ma`akatar lura da babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ta sanar da cewa, ba da jimawa ba za ta fara aikin rushe wasu rukunan gidaje da aka gina ba tare da izini ba a wasu unguwannin dake birnin.

Daraktan sashen lura da bunkasa birnin dake ma’aikatar Muktar Galadima ne ya tabbatar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja, fadar gwamnatin Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya Wakilinmu Garba Abddullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Alhaji Muktar Galadima ya ce, a kai rahotanni da ma’aikatar lura da birnin na Abuja ya samu inda wasu mutane ke amfani da wasu kafofin sada zumunta wajen tallata gidaje na alfarma da suka gina ba tare da izinin mahukunta ba.

Ya ce, irin wadannan gidaje yanzu haka suna ci gaba da kara yawaita a wasu unguwanni dake birni na Abuja, lamarin da yake matukar shafar taswirar birnin.

Alhaji Muktar Galadima ya ci gaba da cewa duk da babu wani tsari a kasa da hukumar bunkasa birnin Abuja ta yi na fitar da filaye a irin wadannan unguwanni, amma kuma abin takaici wasu bata gari sun samar da takardun shedar mallaka na jabu tare da gina gidaje da nufin sayarwa ga jama’a.

Babban daraktan ya ce babu wani taku na fili ko kuma unguwa da hukuma ba ta da tarihinsa a birnin na Abuja, kuma a ko da yaushe ana la’akari da ainihin taswirar bunkasa birnin a duk lokacin da gwamnati ta bukaci gudanar da wani aiki na raya birnin ta hanyar gine-gine ko kuma samar da wasu ababen more rayuwa.

Ya kara da cewa, gwamnati ko kadan ba za ta taba amincewa a lalata mata kyakkyawan tsarin da ta dauko ba na raya birnin na Abuja.

“Shi ya sa muke sanar da jama’a cewa dukkan irin wadannan filaye da gidaje da ake tallata su ba su da shedar amincewar gwamnati.”

Malam Muktari Galadima ha`ila yau ya ce daga yanzu masu wadannan gine-gine su ne za su ringar daukar alhakin biyan kudin aikin rushe ginin da suka yi, sannan kuma daga bisani a gurfanar da su gaban kotu.

“A yanzu haka mun rigaya mu sanya alamomi a irin wadannan gine-gine kuma bada jimawa ba za mu dukufa wajen aikin rushe gine-ginen.”

Yankunan da aikin rushe gine-ginen zai shafa sun hada da hanyar zuwa tashar jirgin kasa dake Idu, da yankin Apo da kuma Lugbe, inda a wadannan wurare ne yanzu haka jama’a ke kashe kudade wajen gina manyan gidaje ba tare da izinin gwamnati ba. (Garba Abdullahi Bagwai)