Sani Abba Garba Maizare: Sinawa mutane ne masu kirki da saukin mu’amala
2023-03-14 15:50:10 CMG Hausa
Sani Abba Garba Maizare, haifaffen Kano ne daga tarayyar Najeriya, wanda ya taba zuwa kasar Sin don yin karatun digiri na biyu a fannin lissafi.
A yayin zantawar sa da Murtala Zhang, Sani Maizare ya waiwayi karatu da rayuwar da ya taba yi a kasar Sin, inda ya bayyana fahimtar sa kan al’adu da halayen mutanen kasar.
A karshe, ya bayyana fatan sa ga ‘yan Najeriya, musamman matasa, wadanda suke son zuwa kasar Sin don yin karatu. (Murtala Zhang)