An rufe wasu bankuna biyu a Amurka
2023-03-14 10:00:06 CMG Hausa
An rufe bankin Silicon Valley Bank (SVB) a ranar 10 ga watan Maris din da muke ciki, wanda ya zama banki mafi girma da aka rufe a Amurka, tun bayan barkewar rikicin hada-hadar kudi a shekara ta 2008. Daga bisani a ranar 12 ga wata, an rufe wani bankin kasar na daban da ake kira Signature Bank, sakamakon “hadarin dake tattare da tsarinsa”.
Sakamakon haka, darajar takardun hannayen jarin bankuna ta fadi warwas, kana tashi da karuwar mizanin cibiyoyin bibiyar kasuwar hannayen jari na Dow Jones, da na Nasdaq, da na S&P 500 sun bambanta sosai, lokacin da aka rufe kasuwannin hannayen jari na kasar.
Rufe manyan bankunan biyu da aka yi a Amurka, ya kuma kawo tangal-tangal a kasuwannin hannayen jarin kasashen Turai, inda a jiya Litinin, babban mizanin wasu muhimman hannayen jari ya sauka matuka, inda raguwar mizanin ya zarce kashi 2 bisa dari. Takardun hannayen jarin bankunan Turai ma sun gamu da mummunar matsala.
Da take jawabi, sakatariyar kudin Amurka, Janet L. Yellen ta ce, babban dalilin da ya janyo rufewar bankin SVB shi ne, kara kudin ruwa babu tsayawa da asusun ajiyar kudaden kasar ya yi, al’amarin da ya jawo babbar raguwar darajar takardun bashin da bankin ke da su. (Murtala Zhang)