logo

HAUSA

Shugabanci Na Gari Shi Ne Sirrin Zaman Lafiya Da Ci Gaban Kasa

2023-03-14 19:28:25 CMG HAUSA

DAGA FA’IZA MUSTAPHA

An rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, bayan an sake zaben Xi Jinping a matsayin shugaban kasar Sin a wa’adi na uku, na shekaru 5.

Jawabin da shugaban ya yi a jiya, ya ja hankalina matuka, inda yake cewa, amincewa da shi da jama’a suka yi, ita ce ke ba shi kwarin gwiwar ci gaba da yin aiki, wanda babban nauyi ne da ya rataya a wuyansa.

Ba shakka, sirrin ci gaban kowacce kasa da ma tabbatuwar zaman lafiya a kasar, shi ne shugabanci na gari. Kuma sai shugaba ya zama nagartacce kafin al’umma su aminta da shi.

Jagorantar mutanen da yawansu ya kai biliyan 1.4, ba karamin abu ba ne. Hausawa kan ce idan dambu ya yi yawa, to ba ya jin mai. Sai dai wannan zance ya sha bambam da yanayin kasar Sin, domin an ga yadda al’ummar kasar da ta zarce yawan na kowacce kasa a duniya, ke rayuwa cikin kwanciyar hankali da lumana da wadata, haka kuma sun kasance masu matukar biyayya ga shugabanninsu tare da amincewa da manufofin da suka gabatar.

Karkashin jagorancin Xi Jinping, kasar Sin ta samu muhimman nasarori da ba a taba gani ba a tarihi, lamarin da jagorancin al’ummar kasar shiga wani sabon babi na ci gaba. Misali, a karkashin shugabancinsa ne kasar Sin ta yi adabo da talauci baki daya, shekaru 10 kafin ma lokacin da MDD ke fata. Haka kuma, jama’ar kasar na more zaman lafiya da kwanciyar hankali da zaman jituwa tsakanin mabanbantan kabilu dake akwai. An kuma ga yadda kasar Sin da ba ta da yawan filayen noma, take iya ciyar da al’ummarta har ma take bayar da gudunmawar abinci ga masu bukata, baya ga yadda kasar ta kai matsayin koli wajen jagorantar duniya a fannonin fasahohin zamani da tattalin arziki da sauransu.

Shugaban ya kara da cewa, zai sadaukar da kansa, kuma zai yi aiki tukuru bisa bukatun kasa, da muradun jama’a.  A ganina, shugaba kasar Sin ya riga ya cika burin al’umma da muradinsu, shi ya sa suka aminta da shi, suke ba shi goyon baya, tare da kara ba shi ragamar mulkin kasar. Ba makawa alkwarin nan da ya yi musu, zai cika shi kamar yadda aka gani a baya. Hakika sake zabensa da Sinawa suka yi, ya tabbatar da cewa, suna son ci gaba da more rayuwa ta jin dadi da sauran al’ummomin duniya ke muradi. Haka kuma, wannan ya tabbatar wa duniya cewa, salon demokuradiyyar kasar Sin, demokradiyya ce ta al’umma domin al’umma.