logo

HAUSA

Xi Jinping: Za a tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ci gaba mai inganci da kuma mai da jama’a a gaban kome

2023-03-13 10:44:37 CMG Hausa

A yau ne aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin a birnin Beijing, majalisar da ta kasance hukumar koli ta kasar. A jawabin da ya gabatar a yayin rufe taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ci gaba mai inganci da kuma mai da jama’a a gaban kome a kokarinta na raya kanta da ma farfado da al’ummar kasar, za ta kuma yi kokarin tabbatar da manufar “kasa daya amma tsarin mulki iri biyu” da ma dinkuwar kasar baki daya, tare da kokarta wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama. (Lubabatu)