logo

HAUSA

Xi Zai Halarci Taron Kolin JKS Da Jam'iyyun Siyasa Na Duniya

2023-03-13 14:51:35 CMG Hausa

Mai magana da yawun sashen yin cudanya da kasashen waje na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Hu Zhaoming ya sanar Litinin din nan cewa, za a gudanar da taron koli na JKS da jam'iyyun siyasa na duniya ranar Laraba ta kafar bidiyo.

Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Sin, zai halarci bikin bude taron daga nan birnin Beijing, tare da gabatar da wani muhimmin jawabi.

Hu ya bayyana cewa, taron mai taken "Tafarkin zamanantarwa: Nauyin dake wuyan Jam'iyyun Siyasa" zai hallara shugabannin jam'iyyu da kungiyoyin siyasa daga kasashe da dama.(Ibrahim)