logo

HAUSA

Xi Jinping: kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga ketare

2023-03-13 10:53:01 CMG Hausa

A yau ne aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin a birnin Beijing, majalisar da ta kasance hukumar koli ta kasar. A jawabin da ya gabatar a yayin rufe taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ci gaban kasar Sin na haifar da alfanu ga duniya, kuma kasar Sin ba za ta iya ware kanta da sauran kasashen duniya wajen tabbatar da ci gabanta ba. Kasar Sin za ta tsaya ga bude kofarta ga duniya, ta yi amfani da kasuwanni da ma albarkatu na duniya don raya kanta, tare kuma da sa kaimin ci gaban duniya baki daya. (Lubabatu Lei)