Xi Jinping: Ba za a ci amanar jama’a ba
2023-03-13 10:08:16 CMG Hausa
Yau Litinin 13 ga wata ne, aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin kolin rundunar sojan kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cikin jawabinsa yayin bikin rufe taron cewa, amincewar da jama’ar suka nuna masa, ta karfafa masa gwiwar neman samun ci gaba, wadda kuma shi ne nauyin da ke wuyansa. Xi ya kara da cewa, zai yi iyakacin kokarinsa wajen ganin ya sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya dora masa. Zai kuma yi aiki tukutu bisa bukatun kasa, da muradun jama’a. Bugu da kari, zai sadaukar da kansa. Ba zai kuma ci amanar wakilan jama’a masu halartar taron da kuma daukacin al’ummomin kabilun kasa ba. (Tasallah Yuan)