Firaministan Sin ya nuna cikakken kwarin gwiwa kan yanayin tattalin arzikin kasar Sin
2023-03-13 12:58:35 CMG Hausa
Sabon firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana da cikakken kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin kasar. Yana mai cewa, za ta magance abubuwan dake neman hana ruwa gudu, don samun kyakkyawar makoma.
Li Qiang ya shaidawa taron manema labarai hakan ne Litinin din nan, bayan kammala taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 14.
Li ya ce, idan har ana fatan cimma burin samun bunkasuwar yawan GDP da ya kai kusan kashi 5 bisa 100 a shekarar 2023, bisa babban tushen da ake samu a fannin tattalin arzikin kasar a halin yanzu, to hakan ba abu ne mai sauki ba, kuma yana bukatar kara zage damtse.
Ya kara da cewa, babban makasudin aikin jam'iyyar da ma gwamnati shi ne, kyautata jin dadin jama'a. Don haka wajibi ne a ko da yaushe gwamnati ta yi shiri tare da gudanar da ayyukanta bisa la’akari da abin da jama’a ke ji da kuma aiwatar da bukatun jama’a. (Ibrahim Yaya)