Ekaterina: Ruhin ra’ayin gina kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil Adama ya burge ni sosai
2023-03-13 20:55:21 CMG Hausa
Daga Belarus zuwa kasar Sin, ita 'yar jarida ce mai aiki a gaba da bayan fage, sannan kuma wakiliyar sada zumunci tsakanin Sin da Belarus da ta sadaukar da kai wajen yin mu'amalar al'adu. Sunanta Ekaterina. A cikin shekaru biyar da take zaune a kasar Sin, ta saba da yadda al'ummar kasar Sin take, ta koyi tarihi da al'adun kasar Sin sosai, ta kuma bayyana labarin kasar Sin sosai, ta hakan ta gina wata karamar gada don sada zumunta a tsakanin kasashen biyu.
A shekarar 2017, a dandalin gasar Sinanci na daliban jami’o’i na kasa da kasa mai taken “Gadar Sinanci”, Ekaterina, 'yar kasar Belarus, ta bayyana burinta a kasar Sin, wannan gasar ta sa ta gane cewa, tana fatan cimma burinta a nan kasar Sin. Game da haka, iyalinta sun goyi bayan zabin ta kuma suna alfahari da ita.
Mahaifiyar Ekaterina ita ma "mai goyon bayan kasar Sin ce", ta bukaci 'yarta ta musamman, da ta dauki akwati fanko zuwa kasar Sin, kuma bayan ta cika shi da ganyen shayi mai kamshi da alawar madara mai tambarin zomo wato alawar “White Rabbit” sai ta mayar da shi zuwa Belarus.
“Mahaifiya ta tana son shan alawar ‘White Rabbit’ sosai, yanzu ina aika babban akwati ga iyayena a kowane zangon karatu, inda nake cikewa da magungunan gargajiya na kasar Sin da suke so, har ma da ganyen shayi na kasar Sin, ban da wannan kuma akwai wasu kayan ciye-ciye irin na kasar Sin.”
Ekaterina ta yi waiwaye cewa, daga koyon Sinanci a kwalejin Confucius da ke Jami'ar Harsuna ta Minsk zuwa halartar gasar “Gadar Sinanci”, koyon Sinanci ya zama abu mai ban sha'awa gare ta.
Daga baya, an ba Ekaterina gurbi a Jami'ar Tsinghua da Jami'ar Peking, wato jami’o’i biyu da suka fi shahara a kasar Sin don yin karatu.
A lokacin da ta yi karatu a kasar Sin, ta sa himma wajen shiga cikin harkokin makaranta da zamantakewa, da sanya kayan gargajiya na kasar Sin don rera wakokin kasar.
Ekaterina ta ce, wadannan wakoki da tufaffi da kayan ado duk sun sa ta ji yadda al'adun Sinawa ke iya hade kayayyaki masu kyau iri daban daban.
A halin yanzu, Ekaterina tana karatu don neman digiri na biyu a fannin tattalin arziki a jami'ar Peking. Zuwa yanzu ta zauna a kasar Sin tsawon shekaru da dama, a cikin wadannan shekarun, ta kai ziyara yankunan daban daban na kasar don ji da ganin irin kokari da gwagwarmayar da Sinawa ke yi.
A yayin da take kokarin kammala aikin nazari game da bunkasuwar tattalin arziki a karkara, Ekaterina ta je kauyen Yuying na lardin Hebei dake arewacin kasar Sin, inda kuma ta sami labarin cewa, ababen more rayuwa a wurin sun kasance baya-baya, kuma tattalin arzikin wurin ya bunkasa sannu a hankali. Amma, yanzu kauyen Yuying ya kawar da talauci, kuma mazaunan kauyen na kara samun wadata, jama’a suna jin dadin zaman rayuwarsu. Ekaterina ta ce,
“Lokacin da na je kauyen Yuying, na ga mazaunansa sun samu ci gaba masu yawa a fannoni da dama kamar na wadatar abinci, tufafi da ilimi da ma lafiya da kwanciyar hankali. Kauyen ya juya daga wani wuri mai fama da talauci sosai a shekaru sama da 20 da suka gabata, zuwa wuri mai aminci da wadata a yanzu. Ban da wannan kuma, kyautattuwar ababen more rayuwa da aka samu a kauyen, sun faranta mazauna kauyen kwarai da gaske, su kan gudanar da wasu ayyuka, ciki har da rera waka, da raye-raye da dai sauransu, wannan ya kasance abun da ya fi burge ni, a gani na, kamata ya yi a yi koyi da haka.”
Baya ga haka, Ekaterina ta taba kai ziyara birnin Yulin na lardin Sha’anxi dake arewa maso yammacin kasar Sin, yadda ake cimma nasarar kawar da talauci a wurin, shi ma ya ba ta mamaki sosai. A karnin da ya gabata, birnin Yulin ya sha fama da guguwar kasa, kuma da wuya a sami hanya mai kyau, a hakika dai mazauna kauyen sun yi zama cikin yanayi mara kyau. Amma, yanzu an gina hanyoyin mota na zamani a kauyen, kuma ana ta kokarin raya masana’antu a wurin.
“Abin da ya ba ni mamaki shi ne, lokacin da muka je birnin Yulin, muna iya ganin bishiyoyi da yawa a kan hanya, lallai ba kamar yadda yake cikin hamada ba. Kana iya ganin ganyyaye da yawa, mazauna wurin suna noman kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa iri-iri, gaskiya a karkashin shugabancin karamar hukumar, zaman rayuwar jama’ar wurin ya samu ingantuwa sosai.”
A shekarar da ta gabata, Ekaterina ta sami karramawa ta kallon bikin budewa da rufe gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta birnin Beijing, inda ta ce hakika ta ji ma'anar ruhi na gina kyakkyawar makomar bai daya ga bil'adama. Ta ce, yanzu muna iya ganin girman kasar Sin da fasaharta ta ci gaba, a sa'i daya kuma, za mu iya jin cewa, kasar Sin tana da ruhin abokantaka, da kirki, tana maraba da mu sosai, ba ta taba tsayawa kan wani wuri mai tsayi don ta raina mu ba. A ganinta, irin annashuwar da ta ji a bikin budewa da rufe gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, ya burge ta.
A wannan zamani da ake samun saurin bunkasuwar fasahar sadarwa ta yanar gizo, Ekaterina ta kan gabatar da nata labarin ga al'ummomin kasashen Sin da Belarus ta kafofin sada zumunta, kana tana fatan nuna wa duniya cikakkiyar kasar Sin. Ta ce,
“Kasar Sin ta fahimci duniya, amma mutane a kasashe da dama na duniya ba sa fahimtar kasar Sin, kuma rahotanni da dama da aka bayar na cike da rashin fahimta da karya. Don haka, na kan wallafa wasu bidiyoyi a dandalin sada zumunta don ba da labarai kan yadda nake karatu da zama a kasar Sin, kuma na kan gabatar da Belarus ga masu amfani da yanar gizo na kasar Sin.”
Ekaterina ta ce, bisa ga karuwar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, jama'ar kasashen biyu za su kara fahimtar juna. Ta ce za ta ci gaba da ba da labarin kasar Sin da na Belarus, don ba da gudummawa wajen zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.