Taron NPC na kasar Sin ya karfafa gwiwar duniya
2023-03-13 21:45:22 CMG Hausa
A yau Litinin aka kammala taron farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin na 14 a birnin Beijing. Kafofin watsa labarai na duniya sun yi imanin cewa, shirin da aka yi na raya kasar Sin ba bayyana alkiblar kasar kadai ya yi ba, har ma da ba duniya kwarin gwiwa.
“Ci gaban kasar Sin zai yi wa duniya amfani, kuma ba za a iya kebe ci gaban kasar daga sauran sassan duniya ba. Ya kamata mu fadada bude kofa, kuma kada mu yi amfani da kasuwar duniya da albarkatu domin raya kanmu kadai, ya kamata mu inganta samar da ci gaba na bai daya a duniya.” Kalaman Xi Jinping sun bayyana dangantakar Sin da duniya, kuma sun bayyana kudurin kasar na ci gaba da fadada bude kofa.
Za a iya sa ran cewa, ta hanyar kasar Sin ta zamanantar da kanta, duniya za ta ci gajiyar ci gaban kasar, haka kuma za a samu karin kwanciyar hankali da kuzari ga zaman lafiyar duniya. (Fa’iza Mustapha)