logo

HAUSA

Kasar Sin wuri ne da ke jawo hankalin baki ’yan kasuwa

2023-03-13 09:52:27 CMG Hausa

Alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a watan Janairun da ya gabata, jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da su, wanda ake juyawa, ya karu da kashi 14.5 bisa 100, idan aka kwatanta da na watan Janairun shekarar 2022 zuwa kudin Sin RMB Yuan biliyan 127.69. Lamarin ya nuna cewa, kasar Sin, wuri ne da ke jawo hankalin baki ’yan kasuwa da su zuba jari da habaka harkokinsu na cinikayya.