logo

HAUSA

Xi Jinping: Za a kara yin yaki da cin hanci da karbar rashawa

2023-03-13 10:41:26 CMG Hausa

 

Yau Litinin 13 ga wata, aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin kolin rundunar sojan kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cikin jawabinsa a yayin bikin rufe taron cewa, yayin da ake raya kasar Sin mai karfi, tilas ne a karfafa raya jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ko da yaushe a tafiyar da harkokin jam’iyyar a tsanake ba tare da kasala ba, kuma a kara yin yaki da cin hanci da karbar rashawa ba kakkautawa. (Tasallah Yuan)