logo

HAUSA

Ta yaya za a taimakawa jarirai su yi barci?

2023-03-13 09:20:34 CMG Hausa

Kullum gazawa wajen taimakawa jarirai su yi barci, yana addabar iyayen da suka haihu ba da dadewa ba. Sabon nazari da aka gudanar a kasar Japan ya bayyana cewa, yayin da jarirai suke kuka, suka kasa yin barci, rungumar su tare da yin tafiya ya fi ba da damar taimaka musu yin barci cikin gajeren lokaci. Rungumarsu cikin mintoci 5 zuwa 8 daga baya a saka su kan gado, ta haka za su ci gaba da yin barci a maimakon farka daga barci. Masu nazari daga wasu hukumomin nazari na kasar Japan sun gudanar da nazarinsu kan jarirai 21 ‘yan kasa da watanni 7 da kuma iyayensu mata, inda suka rubuta yadda suke kasancewa da kuma tattara hotunan binciken bugun zuciyarsu yayin da suke kuka, suka kasa yin barci, iyayensu mata suka rungume su suna tafiya, da rungumarsu suna zauna, da saka su cikin keken jarirai, da kuma dora su kan gado.

Masu nazarin sun gano cewa, yayin da jairan suke kuka suka kasa yin barci da kansu, idan iyayensu sun rumgume su suna tafiya, to, cikin sauki jarirai suke dakatar da yin kuka, kuma bayan mintoci 5, su daina kukan, rabinsu kuma kan yi barci. An gano irin wannan batu a wani nazari da aka gudanar kan daukacin 'ya'yan dabbobi masu renon 'ya'ya da nono a shekarar 2013. Alal misali, yayin da namun daji suke tafiya tare da sanya ‘ya’yansu kan bayansu ko baka ko rungumarsu, ‘ya’yansu ba su yin kuka, su kan kasance cikin nitsuwa, lamarin da zai tabbatar da lafiyarsu duka.

Ban da haka kuma, masu nazarin sun gano cewa, sulusin jariran da suka gudanar da nazarin a kansu su kan farka daga barci cikin gajeren lokaci bayan da aka saka su kan gado. Hotunan binciken bugun zuciyarsu sun shaida cewa, wadannan jarirai sun farka daga barci ne sakamakon saurin bugun zuciya saboda an fara raba su daga jikunan iyayensu mata.

Haka zalika, masu nazarin na kasar Japan sun nuna cewa, idan iyaye sun ci gaba da rungumar jariransu a zaune cikin mintoci 5 zuwa 8 bayan da jariransu suka fara barci, to, jariran su kan yi barci mai zurfi, daga baya idan iyayen suka ajiye jariran a kan gado, jariran ba za su farka daga barci ba.

Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta bayyana ra’ayinta kan muhimmancin sakamakon nazarin, inda ta ce, ana fatan sakamakon nazarin zai taimaka wajen rage matsin lambar da iyaye suke fuskanta wajen renon ‘ya’yansu yadda kamata. (Tasallah Yuan)