logo

HAUSA

Ci gaban tattalin arzikin Sin zai ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya

2023-03-12 16:25:39 CMG Hausa

Taruka biyu wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar na bana, sun ja hankalin al’ummun kasa da kasa matuka, inda masanan tattalin arzikin duniya ke ganin cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. Masanan sun kuma bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana sanya moriyar al’ummar kasa a gaban komai yayin da take kokarin raya tattalin arzikin kasa, don haka ya dace a koyi darrasin kasar na raya kasa.

Mataimakin shugaban majalisar wakilai na kasar Afirka ta kudu, Lechesa Tsenoli ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi nasarar kawar da talauci bisa matsayinta na babbar kasa, lamarin da ya zama abun koyi ga sauran kasashen duniya.

Kana babban sakataren kungiyar sada zumunta tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa ta kasar Sudan, Ali Yusuf ya yi tsokaci cewa, abun da ya fi jan jankalin kasashe masu tasowa shi ne, shawarar ziri daya da hanya daya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, saboda ta warware matsaloli da dama da suke fuskanta. (Jamila)