logo

HAUSA

MDD ta jaddada muhimmancin zaben wajen cimma zaman lafiya a Libya

2023-03-12 16:55:14 CMG Hausa

Manzon musammam na sakatare janar na MDD a Libya, Abdoulaye Bathily, ya jaddada muhimmancin da gudanar da zabuka a kasar Libya ke da shi wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaba a kasar.

Abdoulaye Bathily ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai kan kwamitin gudanar da zabe a kasar.

A cewarsa, ba al’ummar Libya damar zaben shugabannin da suke so ta hanyar kada kuri’a, ba makawa, ita ce hanyar samun zaman lafiya da ci gaba da kwanciyar hankali a kasar. Ya ce ana bukatar zabuka domin dawowa da sake gina hukumomin gwamnati da za su wakilta tare da hidimtawa al’ummar kasar.

Har ila yau, ya ce shirye-shirye na riko da gwamnatocin rikon kwarya da suka ki karewa da majalisun dokoki da wa’adinsu ya kare, su ne tushen rashin zaman lafiya dake hadari ga makomar kasar. (Fa’iza)