logo

HAUSA

Xi ya halarci zama na 5 na taron NPC

2023-03-12 20:07:47 CMG Hausa

Da safiyar yau Lahadi ne majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 ta gudanar da zama na 5, na taronta na farko, inda Xi Jinping tare da sauran shugabannin kasar suka halarta.

Da misalin karfe 9 na safiyar gobe Litinin ne za a rufe taron majalisar, a dakin taron al’umma dake Beijing, inda shugaban kasar Sin, Xi Jinping zai gabatar da jawabi.

Bayan rufe taron ne kuma firaminista Li Qiang zai kira wani taron manema labarai na ciki da wajen kasar, domin amsa tambayoyinsu. CMG zai watsa wannan taro kai tsaye a tashoshi daban daban. (Fa’iza Mustapha)