logo

HAUSA

Sharhi: Mene ne ainihin dimokuradiyya?

2023-03-12 22:45:17 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

“Babban nauyin da ke bisa wuyana shi ne in jagoranci mazauna kauyenmu don tabbatar da samun ci gaba da wadatar kauyen”, furucin malam Long Xianwen ke nan dan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin.

Long Xianwen ya fito ne daga kauyen Niujiaoshan da ke yammacin lardin Hunan na kasar Sin, inda ‘yan kabilar Miao ke rayuwa. Yau shekaru sama da 10 da suka wuce, kauyen ya kasance mai talauci, inda matsakaicin kudin shigar da mazaunansa suke samu a shekara bai kai kudin Sin yuan 800 kwatankwacin dala 115 ba. Har ma akwai wakar da ‘yan kabilar Miao kan rera a wurin da ke cewa, “kada mata su auri mazan kauyen Niujiaoshan, inda ake fama da talauci, kuma daga cikin maza 10, 9 sun kasance gwagare.”

Amma yanzu kauyen ya samu matukar gyaran fuska, inda a karkashin jagorancin Long Xianwen, mazauna kauyen suka yi amfani da albarkatun da suke da su, suka fara noman bishiyoyin ganyen shayi a duwatsu, baya ga bunkasa harkokin yawon shakatawa, matakin da ya sa cikin shekaru sama da 10, aka fitar da kauyen daga kangin talauci, inda matsakaicin kudin shigar mazaunasa ya karu da sau 18. A matsayinsa na jagoran kauyen, Long Xianwen ma ya samu goyon baya sosai daga mazauna kauyen, har ma an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin har sau biyu a jere tun daga shekarar 2018. A matsayinsa na dan majalisar, Long Xianwen kusan ya tafi kowane sashe na karkarar yankin yammacin lardin Hunan, kuma ta hanyar ziyartar al’umma da sauraron ra’ayoyinsu da gudanar da bincike, ya fahimci ainihin matsalolin da suke fuskanta, tare da bayyana ra’ayoyi da ma shawarwarinsu a wajen taron majalisar wakilan jama’ar kasar, ta yadda gwamnatin kasar za ta samu damar fahimtar matsalolin da al’ummarta ke fuskanta.

A hakika, Long Xianwen na daga cikin ‘yan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 da gaba dayansu suka kai 2977, wadanda suke gudanar da aikinsu don bauta wa al’ummar kasar. A kasar Sin, ban da ‘yan majalisar wakilan jama’a a mataki na kasa, akwai kuma ‘yan majalisar wakilan jama’a a matsayin larduna da birane da gundumomi da garuruwa, wadanda suke wakiltar al’umma ‘yan kabilu daban daban da ma mabambantan yankuna da sana’o’i. ‘Yan majalisar a matakai daban daban sun bayyana ra’ayoyin al’umma da sa ido a kan yadda gwamnati ke tafiyar da harkoki da kuma sa kaimin warware matsalolin da al’umma ke fuskanta a turbar dimokuradiyyar al’umma baki daya.

A ganin gwamnatin kasar Sin da al’ummarta, dimokuradiyya ba ado ba ne, hanya ce ta warware matsalolin da al’umma ke fuskanta, kuma dimokuradiyya na da mabambantan salo a kasashe daban daban bisa yanayin da suke ciki. Kasancewar kasar Sin kasa mai fadi wadda ke da mafi yawan al’umma a duniya, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta hada gwiwa da sauran jam’iyyun siyasa na kasar, suka gano hanyar dimokuradiyyar da ta dace da yanayin da take ciki.

Jama’ar wata kasa ne suke da ‘yancin tabbatar da ko kasar na kan tafarkin dimokuradiyya ko a’a.  Binciken sauraron ra’ayoyin al’umma ya shaida cewa, cikin ‘yan shekarun baya, gwamnatin kasar Sin ta kiyaye sama da kaso 90% na amincewar da al’ummarta suka nuna mata, lamarin da ya shaida ingancin dimokuradiyya a kasar Sin.(Mai Zane:Mustapha Bulama)