logo

HAUSA

Angola za ta tura sojoji domin wanzar da zaman lafiya a DRC

2023-03-12 16:58:12 CMG Hausa

Kasar Angola ta sanar da cewa, za ta tura dakaru domin taimakawa ayyukan wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, bayan tuntubar hukumomin kasar.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin shugaban kasar Angola a kafar Facebook, jiya Asabar, ta bayyana cewa, aikin dakarun shi ne kame sansanonin mayakan M23 da kare mambobin kwamitin wanzar da zaman lafiya a yankin gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Sanarwar ta kara da cewa, Angola ta sanar da shugabannin shiyyar game da wannan batun, karkashin shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin Angolar da Kenya wato “The Luanda and Nairobi Processes”, da MDD da Tarayyar Afrika da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika wato ECCAS.

Har ila yau, sanarwar ta ce shugaban kasar Angola, kuma shugaban rundunar sojin kasar, zai nemi izinin majalisar dokokin kasar domin tura sojojin. (Fa’iza)