logo

HAUSA

Saudiyya Da Iran Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Dawo Da Huldar Jakadanci Tare Da Sake Bude Ofisoshin Jakadanci A Tsakaninsu

2023-03-11 15:32:11 CMG Hausa

Kamar yadda kasashen Sin da Saudiyya da Iran suka sanar a ranar Jumma’ar da ta gabata, kasashen biyu wato Saudiyya da Iran, sun cimma matsaya, wadda ta hada da yarjejeniyar dawo da huldar jakadanci da ma sake bude ofisoshin jakadanci da sake tura jakadu a tsakaninsu cikin watanni biyu.

Karamin ministan harkokin wajen kasar Saudiyya, kuma memba a majalisar ministocin kasar, kana mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Musaad bin Mohammed Al-Aiban, shi ne ya jagoranci tawagar kasar ta Saudiyya, yayin da sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran, Admiral Ali Shamkhani ya jagoranci tawagar kasar Iran a lokacin tattaunawar da ta gudana a birnin Beijing, fadar mulki kasar Sin daga ranakun 6 zuwa 10 ga watan Maris, kamar yadda wata sanarwar bangarorin uku da suka hada da kasashen Sin, Saudiyya da Iran suka bayyana.

Sanarwar ta ce, kasashen Saudiyya da Iran duk sun mika godiyarsu ga kasashen Iraki da Oman, bisa daukar nauyin gudanar da shawarwari da dama tsakanin shekarar 2021 zuwa ta 2022, da kuma shugabanni da gwamnatin kasar Sin da suka dauki nauyin gudanar da shawarwarin, gami da goyon baya da kuma gudummawar da ta kai ga samun nasarar shawarwarin.

Yayin da yake taya bangarorin biyu murnar daukar wani mataki na tarihi, daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan bangarorin biyu wajen samun ci gaba mai inganci kamar yadda aka cimma cikin yarjejeniyar, ta yin aiki don samun kyakkyawar makoma tare da yin hakuri da nuna hikima.

Ita ma MDD ta yi maraba da wannan yarjejeniya da kasashen Saudiyya da Iran din suka cimma ta sake farfado da huldar diflomasiyya a wannan rana, kana ta yaba da rawar da kasar Sin ta taka a wannan lamari. Bugu da kari, kasashen Oman, da Türkiye, da Lebanon, da Iraki da sauran kasashe, sun fitar da sanarwa, inda suka yi maraba da sanarwar hadin gwiwa da bangarorin uku suka fitar.(Ibrahim)