logo

HAUSA

Mai Magana Da Yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ya Yi Karin Haske Kan Tattaunawar Saudiyya Da Iran

2023-03-11 21:14:08 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya yi tsokaci kan tattaunawar da aka yi tsakanin kasashen Saudiyya da Iran a nan birnin Beijing, wanda ya samu kulawa sosai daga bangarori daban-daban.

Kakakin ya ce, tare da hadin gwiwar bangarorin da abin ya shafa, tattaunawar da aka yi tsakanin kasashen na Saudiyya da Iran a birnin Beijing, ta haifar da kyakkyawan sakamako. Kasashen Saudiyya da Iran sun fitar da taswira da kuma lokacin da za a bi, wajen kyautata hadin gwiwarsu, wanda ya samar da wani ginshiki mai kyau, na ciyar da hadin gwiwarsu gaba da kuma sake bude wani sabon babi a huldarsu.

Kakakin ya jaddada cewa, kasar Sin ba ta nuna son kai ko kadan a yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa, kasar Sin na mutunta matsayin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, kasancewar wannan yanki nasu ne, kuma tana adawa da gasar siyasa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ba ta da wata niyya, kuma ba za ta nemi cike wani gurbi ba, ko kuma kafa kungiyoyi na musamman, yana mai cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana ganin cewa, ya kamata a ko da yaushe, makomar yankin Gabas ta Tsakiya ta kasance a hannun kasashen yankin. (Ibrahim)