logo

HAUSA

An rufe zaman farko na majalisar CPPCC karo na 14

2023-03-11 17:10:56 CMG Hausa

An rufe zaman farko na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin ko kuma CPPCC a takaice karo na 14 da maraicen yau Asabar 11 ga wata.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran wasu shugabannin kasar, sun halarci bikin rufe taron da ya gudana a babban dakin taron al’umma dake Beijing, fadar mulkin kasar.

Shugaban kwamitin majalisar CPPCC karo na 14, Wang Huning, ya jagoranci bikin rufe taron tare da gabatar da jawabi.

A yayin zaman taron, an zartas da wasu kudirori, ciki har da kudiri kan rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar CPPCC karo na 13, da kudiri kan rahoto game da shawarwarin da masu ba da shawarwarin siyasa suka bayar, da kudiri kan gyaran kundin ka’idojin majalisar, da rahoto kan duba sabbin shawarwarin da aka bayar, gami da wani kudirin siyasa game da zaman farko na kwamitin majalisar CPPCC karo na 14. (Murtala Zhang)