logo

HAUSA

Gwamnatin Sin ta ba da tallafin hatsi ga Saliyo

2023-03-10 14:01:40 CMG Hausa

An gudanar da bikin mika hatsin da gwamnatin kasar Sin ta bada a matsayin tallafin gaggawa ga kasar Saliyo a jiya Alhamis.

Yayin bikin wanda ya gudana a zahiri da kuma ta yanar gizo, babban jami’in hukumar kula da ci gaba da hadin gwiwar kasashen duniya ta kasar Sin ya bayyana cewa, samar da isashen hatsi muhimmin abu ne game da tafiyar da harkokin mulkin kasa, kuma abu ne da ajandar ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030 ta MDD ta fi damuwa da shi.

Game da hatsin da ake bukata cikin gaggawa a Afirka, Sin tana son ba da taimako cikin sahihanci ga kasashen Afirka. Inda zuwa yanzu, aka riga aka yi sufurin dukkan tallafin hatsin cikin gaggawa ga Afirka da gwamnatin Sin ta sanar. Tallafin ya riga ya isa kasashen Guinea-Bissau, da Saliyo da sauran wasu kasashe daya bayan daya.

Mataimakin shugaban hukumar kula da ci gaba da hadin gwiwar kasashen duniya ta kasar Sin Tang Wenhong ya bayyana cewa, ba ma kawai ba da tallafin hatsi cikin gaggawa ga Afirka Sin ta yi ba, har ma da taimaka wa kasashen Afirka wajen neman ci gaban aikin gona mai dorewa ta hanyoyin gina cibiyoyin aikin gona, da gudanar da hadin gwiwa kan fasahohin zamani da kuma horar da ma’aikata da dai sauransu. A cewarsa, bangaren Sin zai ci gaba da ba da tallafi ga Afirka, kamar taimakawa gina manyan ababen more rayuwa na aikin noma, da samar da fasahar noman irin shinkafa da aka tagwaita da ciyayin samar da laimar kwado da sauran shuke-shuken dake dacewa da yanayin Afirka. Sannan za ta ci gaba da tura masana aikin noma, da karfafa horar da karin ma’aikata da sauransu, ta yadda za a iya taimakawa Afirka wajen gina tsarin aikin noma mai bin fasahohin zamani. (Safiyah Ma)