logo

HAUSA

Memban majalisar CPPCC Shi Weidong: Ya dace a yi kokarin zamanantar da harkokin kere-keren kasar Sin

2023-03-10 22:23:36 CMG Hausa

A cikin rahoton aikin gwamnatin da firaminista Li Keqiang ya gabatar a wajen zaman farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) karo na 14, alkaluman da aka bayar sun shaida dimbin nasarorin da kasar ta samu a shekarar da ta gabata. Kana, rahoton ya jaddada cewa, kamata ya yi a samar da ci gaba ta hanyar da ta dace, da aiwatar da manufofi masu dorewa, domin samar da ci gaba mai inganci. Yadda za’a yi domin yin kokarin samar da ci gaba mai inganci, ya zama wani muhimmin batun da ya ja hankalin wakilan majalisar NPC, gami da membobin majalisar CPPCC, wato majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar.

Shi Weidong, daya ne daga cikin membobin majalisar CPPCC karo na 14, kana shugaban jami’ar Nantong dake lardin Jiangsu na kasar Sin, wanda ya dade da maida hankali kan bunkasa ayyukan kere-kere bisa fasahohin zamani. A bana, Shi ya gabatar da wata shawara game da raya tattalin arziki irin na zamani, da kara zamanantar da ayyukan kere-keren kasar Sin.

Shi ya ce, zamanantar da harkokin kere-kere, na bukatar kokari a fannoni da dama, ciki har da fasahohi, da kere-kere, da kiyaye muhalli, da makamashi, da mu’amala da kasashen waje da sauransu. Ya bada shawarwari a wasu fannoni uku. Na farko, horas da kwararru, don bada tabbaci ga samar da ci gaba mai inganci. Na biyu, zurfafa binciken ilimi daga tushe, don bada karfin yin kirkire-kirkire ga samar da ci gaba mai inganci. Na uku shi ne, kara yin kirkire-kirkire, don samar da tallafin kimiyya da fasaha ga ci gaba mai inganci. (Murtala Zhang)