logo

HAUSA

Jami'in Najeriya: Inganta samun wadata tare zai samar da karin kuzari ga ci gaban kasar Sin

2023-03-10 10:41:36 CMG Hausa

A yayin manyan tarrukan biyu wato na NPC da CPPCC da har yanzu ake gudanarwa a nan birnin Beijing, nasarorin ci gaban da kasar Sin ta samu a shekarun baya-bayan nan na ci gaba da jan hankalin bangarori daban daban a nahiyar Afirka. A yayin da yake zantawa da manema labaru na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, karamin ministan ayyuka da gidaje na Najeriya Umar El-Yakub ya bayyana cewa, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar, wata shawara ce da ta sa kaimi ga rugujewar shingen ciniki, da inganta mu'amalar al'adu daban-daban, da tallafawa raya ababen more rayuwa a duniya, wadda ta samu karbuwa a kasashen Afirka, yana mai cewa, Najeriya tana daya daga cikinsu. A cewarsa, ta hanyar hadin gwiwar “Ziri Daya da Hanya Daya”, wasu ayyukan samar da ababen more rayuwa a Najeriya sun samu kudi, baya ga haka kamfanonin kasar Sin sun samar da fasahohin zamani a wurin, inda y ace wadannan ayyuka za su ci gaba da amfanar Najeriya.”

Umar El-Yakub ya kara da cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta yi nasarar yaki da talauci kamar yadda aka tsara, tare da karfafawa da fadada sakamakon kawar da fatara, wanda ya ba da mamaki ga duniya. Ya ce ya yi imanin cewa, dagewar da kasar Sin ta yi kan inganta samun wadata tare, zai ba da himma wajen samun ci gaba mai dorewa.

Bugu da kari, Umar El-Yakub ya kuma yabawa manufar zamanintarwa iri ta kasar Sin da kasar lalubowa. A ganinsa, neman hanyar ci gaba ta zamani da ta dace da kasa, batu ne da ya kamata kowace kasa ta yi tunani a kai, kuma yana fatan tsarin zamanantar da kasar Sin zai iya kawo karin haske ga duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)