logo

HAUSA

Kwalejin horas da harkokin tsaro na UAE zai hada karfi da Najeriya a fannin al’adu da yawon bude idanu

2023-03-10 09:18:36 CMG Hausa

A ranar Alhamis 9 ga wata, daliban kwalejin horas da dakarun tsaron hadaddiyar daular Larabawa UAE suka ziyarci hedikwatar majalissar lura da al’adu ta tarayyar Najeriya, inda suka kara jaddada bukatar kyautata alaka ta fuskar al’adu da yawon bude idanu a tsakanin kasashen biyu.

Daliban ’yan rukunin karatu na 10 sun ziyarci Najeriya ne a wani bangare na jerin darussan da ake ba su horo, akai a fannin da suka shafi al’adu, yawon bude idanu da kuma raye-raye da wake-wake.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Da yake jawabin, jagoran ayarin daliban Col. Mubarak Mohammed Hassan Al-Zaabi ya ce, kamar yadda yake kunshe cikin manhajar tsarin karatun kwaleji, ana baiwa dalibai damar zuwa kasashe daban daban na duniya domin musayar ilimi a fannonin da suka shafi al’adu da kuma diplomasiyya.

Ya ci gaba da cewa sun zo ne Najeriya domin su gudanar da bincike a kan bangarorin da kasashen biyu za su amfani juna sannan kuma a tattauna kan dabarun tabbatar da zaman lafiya a duniya baki daya.

Col Mubaral Al-Zaabi ya ce, Najeriya ta kasance kasa mafi muhimmanci ga daliban, musamman ma a kan abubuwan da suka shafi al’adu kasancewa duk da banbance-banbancen al’adu da ake da su a kasar, amma kuma ta ci gaba da yin fice a fagen bunkasar tattalin arziki a tsakanin kasashen dake nahiyar.

Ya ce daliban za su samu damar yin nazari sosai a ka hanyoyi da dabarun da mahukuntan Najeriya ke bi wajen mancewa da banbance-banbance al’adu domin tunkarar ci gaban kasa, inda ya ce babu shakka daliban za su karu sosai daga irin nazarin da za su yi, sannan kuma sakamakon da suka samu zai taimaki Najeriya da kuma hadaddiyar daular Larabawa.

A lokacin da yake nasa jawabin, Darakta-janar na majalissar raya al’adu ta tarayyar Najeriya Mr Otunba Segun Run-sewe farin cikin sa ya bayyana bisa zabar Najeriya da kwalejin ta yi, inda ya ce ziyarar za ta kara bude kofar musayar al’adu da sauran fannoni a tsakanin kasashen biyu.

Ya ce, abu ne da ya dace matuka baya ga samun kwarewa kan harkokin da suka shafi tsaro, a rinka baiwa sojoji ilimi a bangarorin da suke da nasaba da al’adu da harkokin yawon bude idanu na kasashe daban daban.

“Abin da wanann ziyara take nunawa shi ne baya ga kyakyyawar fahimta ta al’adu dake tsakanin Najeriya da hadaddiyar daular Larabawa, haka kuma akwai alaka ta tsaro da horas da sojoji wanda wannan abin farin ciki ne matuka.”

Daga karshe ya yi alkawarin baiwa daliban cikakken hadin kai da goyon bayan a iya lokacin da za su shafe a Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)