logo

HAUSA

Basiniya Dake Dukufa Kan Raya Al’adun gargajiya Don Ingiza Bunkasuwar Kauyuka

2023-03-10 11:20:47 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, yau ranar mata ta duniya ce, a nan kasar Sin, mata na wani muhimmin matsayi a cikin al’umma. Shi ya sa yau na zana wata mace da ake girmamawa. Sunan wannan mata dake sana’ar dinki Qiao Jinshuangmei, ‘yar kabilar Yi ce, wadda kuma ita ce shugabar gamayyar kungiyar masu sana’ar dinki ta gundumar Mabian mai cin gashin kanta ta kabilar Yi dake birnin Leshan a kudu maso yammancin kasar Sin. Wannan kungiya ta horar da mutane fiye da 3000 aikin dinki irin na kabilar Yi, da ma taimakawa mata sama da 800 masu aikin dinki samun aikin yi. Kokarinta ya kuma taimaka wajen shigar da wannan fasaha cikin sunayen al’adun gargajiya da aka gada daga kaka-kakanni a lardin na Sichuan.

Qiao Jinshuangmei tana kuma da wata matsayi na daban, wato ‘yar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin. A gun taron shekara shekara na majalisar da ke gudana a birnin Beijing, babban birnin kasar, ta bayyana labarinta game da yadda aka raya fasahar dinki ta gargajiya da kuma amfani da ita wajen jagorantar mazauna karkara wajen samun aikin yi da ingiza bunkasuwar kauyuka. Ta ce, za ta yi kokarin kara fito da muryoyin al’umma wurin taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da ke gudana yanzu haka a birnin Beijing, hedkwatar kasar, tare da ba da shawarwari game da bunkasa harkokin al’adu da yawon shakatawa ta yin amfani da fasahar dinkin hannu ta kabilar Yi.

Matan kabilar Yi sun kan dinka abubuwan dake bayyana kyakkyawar fatansu a kan tufafi da hula da takalma, kuma wadannan abubuwa masu kyaun gani sun taimaka musu wajen biyan bukatunsu na yin rayuwa mai dadi. Sinawa na alfahari da al’adunsu, kuma habaka al’adun al’umma na iya ingiza bunkasuwar kauyuka. (Mai zana da rubuta: MINA)