logo

HAUSA

Mambobin CPPCC sun tattauna kan batun samar da ci gaba mai inganci

2023-03-10 10:55:59 CMG Hausa

Ta yaya kasar Sin za ta inganta ci gaba mai inganci a bana? ’Yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin wato CPPCC da ke halartar zaman farko na majalisar karo na 14, sun yi zazzafar muhawara kan wannan batu.

A bana, kasar Sin ta sanya burin samun ci gaban tattalin arziki da kimanin kashi 5 cikin dari. A cewar Han Baojiang, ‘dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, kuma darektan sashen koyarwa da bincike kan harkokin tattalin arziki na kwalejin kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, irin wannan burin ci gaban tattalin arziki yana dacewa da halin da kasar Sin take ciki. Ya ce, bisa tsarin tattalin arzikin kasar Sin, tabbatar da samun karuwar tattalin arzikin na kashi 1 cikin 100, zai iya samar da ayyukan yi kimanin miliyan 2.4, don haka, idan aka tabbatar da karuwar tattalin arzikin na kusan 5%, za a iya samar da ayyukan yi miliyan 12 da kasar ta tsara a shekara mai zuwa.

A nasa bangaren, mataimakin darektan kwamitin kula da tattalin arziki na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin Ma Jiantang, ya yi nuni da cewa, idan ana fatan fadada bukatun cikin gida, kamata ya yi a yi duk mai yiwuwa wajen daidaita kasuwannin tattalin arziki da kuma samun kudin shiga ga jama'a, da amfani da hanyar karbar haraji don rage gibin kudin shiga da jama’ar kasar ke samu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)