logo

HAUSA

Layin Dogo Da Ya Hada Habasha Da Djibouti Da Sin Ta Gina Ya Samu Yabo Yayin Da Yake Cika Shekaru 5 Da Fara Aiki

2023-03-10 20:57:21 CMG Hausa

Layin dogo da ya tashi daga Addis Ababa zuwa Djibouti da kasar Sin ta gina, ya samu yabo bisa yadda ya bunkasa dunkulewar yankin da haifar da nasarori, yayin da yake cika shekaru 5 da fara aiki.

Wannan na zuwa ne yayin da manyan jami’an gwamnatocin Habasha da Djibouti da jami’an diflomasiyya na kasar Sin dake Habasha da ma’aikatan da suka shimfida layin dogon mai tsawon kilomita 752, suka yi bikin cikarsa shekaru 5 a tashar jiragen kasa ta Lebu dake wajen birnin Addis Ababa na Habasha.

Ministan kudi na kasar Habasha Ahmed Shide, ya bayyana yayin bikin cewa, cikin shekaru sama da 5 da suka gabata, layin dogon ya samu dimbin ci gaba a bangarorin da suka shafi gudanawa da kulawa da karfin aiki. Ya kuma yabawa muhimmiyar rawar da yake takawa wajen bunkasa cinikayyar a fannin shige da fice da ma dangantaka tsakanin mutanen kasashen makwabta da fasahohin da ya kai da ma hadin gwiwa tsakanin masana Sinawa da na cikin gida. 

A nasa bangare, ministan sufuri na Habasha, Denge Boru, ya ce layin dogon na yi wa kasashen biyu amfani wajen inganta tattalin arziki da hade al’ummominsu, da saukaka cinikayya da raya masana’antu da samar da damarmakin ayyukan yi da na sana’o’i ga al’ummomin kasashen biyu. (Fa’iza)