Babban jami’in kasar Sin ya tattauna da mambobi masu bada shawara kan harkokin siyasa daga Hongkong da Macao
2023-03-09 14:19:38 CMG Hausa
Babban jami’in kasar Sin Wang Huning, ya tattauna da masu bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin daga yankunan musamman na Hongkong da Macao, yayin zama na farko na kwamitin majalisar bayar da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin karo na 14.
Wang Huning, wanda mamba ne na zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya yi kira da a karfafa tabbacin da ake da shi na raya yankunan na musamman guda biyu da ma kasar baki dayanta, tare da ba yankunan damar taka cikakkiyar rawa wajen inganta farfadowar kasar Sin ta kowacce fuska, ta hanyar zamanantarwa irin na kasar.
Wang Huning ya kuma jadadda muhimmancin aiwatar da cikakkiyar manufar “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu”, wadda a karkashinta al’ummomin yankunan biyu ke tafiyar da harkokinsu da kansu a wani mataki na cin gashin kai. (Fa’iza Mustapha)