Taruku 2 Na Kasar Sin: A Kara Fahimtar Cikakken Tsarin Demokuradiyya Da Ake Damawa Da Jama'a
2023-03-09 21:36:28 CMG Hausa
Yanzu haka ana gudanar da taruku 2 wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, tarukan da suka taimakawa kasashen duniya kara fahimtar cikakken tsarin demokuradiyya da ake damawa da jama'a a kasar Sin.
Yadda aka shimfida demokuradiyya a kasa, ya dogara da yadda jama’ar kasar suka tafiyar da harkokinsu da kansu. Akwai mutane fiye da biliyan 1.4 a nan kasar Sin, adadin da ya kai kusan kashi 1 cikin kashi 5 na jimillar yawan mutanen duniya. To ta yaya mutane masu yawan haka za su bayyana ra’ayoyinsu yadda ya kamata? Ta yaya za su cimma daidaito? Ta yaya za a aiwatar da ra’ayi daya da suka cimma? Kasar Sin ta lalubo bakin zaren daidaita batutuwan, wato cikakken tsarin demokuradiyya da ake damawa da jama'a.
Wannan tsarin na demokuradiyya ya shafi matakan yin zaben, shawarwari, tsai da kuduri, kula da harkoki da sa ido, ta yadda za a saurari ra’ayoyin jama’a da bayyana burikansu a harkokin siyasar kasar Sin da ma zamantakewar al’ummar kasar, lamarin da aka ayyana shi a matsayin tsarin “demokuradiyya mafi shafar kowa, da amfani, kuma ba tare da rufa-rufa ba”.
Demokuradiyya, ba kayan ado ba ne, abu ne da ake amfani da shi domin warware matsalolin da ke addabar jama’a. Ba a raba raya al’umma mai matsakaiciyar wadata ta kowacce fuska, samun gaggarumar nasara wajen dakile da kandagarkin annobar cutar COVID-19, rika zamanintar da kasar Sin da sauran nasarorin da kasar Sin ta samu ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki, daga cikakken tsarin demokuradiyya da ake damawa da jama'a ba. Rahotanni daga shahararrun hukumomin jin ra’ayoyin jama’a na kasa da kasa sun nuna cewa, gamsuwar da jama’ar Sin suka nuna wa gwamnatinsu ya wuce kaso 90 a shekaru baya-bayan nan, lamarin da ya shaida cewa, demokuradiyya irin na kasar Sin na da kuzari sosai. (Tasallah Yuan)