logo

HAUSA

Shugaban jam’iyyar PNDS-Tarayya ya gana da wata tawagar mambobin jam’iyyar PCC ta kasar Sin

2023-03-09 09:13:51 CMG Hausa

A yanzu haka wata tawagar dake kunshe da mambobin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin PCC na ziyarar aiki domin karfafa dangantakar huldar abokantaka da sada zumunci tare da takwarorinsu na jam’iyyar PNDS-Tarayya, inda a ranar 8 ga watan Maris, tawagar a karkashin jagorancin Wang Heming ta gana da Foumakoye Gado, shugaban jam’iyyar PNDS-Tarayya a birnin Yamai.

Daga birnin Yamai din, wakilin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Shugaban kwamitin zartarwa na jam’iyyar PNDS-TARAYYA, Foumakoye Gado, ya gana a yau da safe 8 ga watan Maris din shekarar 2023 a nan birnin Yamai tare da tawagar mambobin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a karkashin jagorancin Wang Heming, jami’in shiyyar Afrika na sashen kasa da kasa na hulda tare da jam’iyyar PCC. Ita dai wannan ganawa na cikin tsarin karfafa huldar dangantaka, da abokantaka tsakanin PNDS-TARAYYA da PCC, kuma wannan rangadi ya kasance na farko tun bayan annobar Covid-19 da wata tawagar jam’iyyar PCC ta kawo a nahiyar Afrika.

Jam’iyyar PCC ta jaddadawa shugaba Foumakoye Gado murnarta bisa ga zaben da aka masa a matsayin shugaban kwamitin zartarwa na PNDS-Tarayya a karshen babban taron jam’iyyar karo na 8 da ya gudana a cikin watan Disamban da ya gabata a birnin Yamai.

Shugaban tawagar kasar Sin, Wang Heming ya bayyana farin cikinsa game da abin da yake gani na kama hanyar ci gaba da kasar Nijar ta runguma, ta dalilin haka, jam’iyyar PCC na fatan cigaba da karfafa huldar dangantaka tare da jam’iyyar PNDS-Tarayya, wuce nan ma tare da Nijar baki daya.

Duk dai cikin tsarin dangantakar dake tsakanin jam’iyyun siyasar biyu, shugaba Foumakoye Gado ya sake tunatarwa domin bayyana gamsuwarsa na ambato dukkan ayyuka da abubuwan da PNDS-Tarayya ta aiwatar tare da taimako da gudunmuwar jam’iyyar PCC.

Har ila yau, bangarorin biyu sun jaddada fatansu na ci gaba da fadada irin wadannan haduwa a tsawon lokacin da wannan rangadi zai dauka, a cewar manyan jami’an biyu na PNDS-Tarayya da PCC.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI, daga Yamai a jamhuriyar Nijar.