logo

HAUSA

Tawagar likitocin kasar Sin ta 20 dake Zimbabwe ta gudanar da bikin kama aiki

2023-03-09 20:10:45 CMG Hausa

A jiya ne, aka yi bikin mika aiki daga tawagar likitoci ta kasar Sin dake kasar Zimbabwe karo na 19 zuwa ta 20 a birnin Harare, babban birnin kasar, inda mukaddashin jakadan Sin dake Zimbabwe Cheng Yan da mataimakin shugaban Zimbabwe kuma ministan kiwon lafiyar kasar Constantino Chiwenga suka halarci bikin.

A yayin bikin, a madadin gwamnatin Zimbabwe, minista Chiwenga ya ba da lambar yabo ga hukumar kiwon lafiya ta lardin Hunan na kasar Sin, wadda ta dauki nauyin tura tawagogin likitoci ga Zimbabwe tsawon shekaru 38.

Chiwenga ya bayyana cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 60 da kasar Sin ta tura tawagar likitoci zuwa kasashen waje. Gwamnatin kasar Sin ta nuna goyon baya ga Zimbabwe wajen inganta sha’anin kiwon lafiyar al’ummar kasar, kana Zimbabwe tana son raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakaninta da Sin, tana kuma fatan ci gaba da zurfafa hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya tsakaninta da Sin don amfanawa jama’arsu baki daya.

Tun daga shekarar 1985 zuwa yanzu, Sin ta tura tawagogin likitoci 19 zuwa Zimbabwe, tare da kula da marasa lafiya fiye da dubu 67 a Zimbabwe. (Zainab)