logo

HAUSA

Wang Huning ya halarci taron wakilan Taiwan

2023-03-09 21:01:03 CMG Hausa

 

Mamban zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Wang Huning, ya halarci taron dudduba rahoton ayyukan gwamnatin kasar tsakanin wakilan jama’a da suka fito daga yankin Taiwan na kasar Sin, wadanda suke halartar zaman taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 14 da safiyar Alhamis din nan a birnin Bejing, fadar mulkin kasar Sin.

Wang Huning ya ce, ya kamata mu aiwatar da cikakken ruhin babban taron wakilan JKS karo na 20, da kiyaye dukkan dabarun jam'iyyar, don warware batun yankin Taiwan a sabon zamani, da martaba ka'idar “Sin daya tak a duniya”, da matsayar da aka cimma a shekarar 1992, da inganta alakar gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, ta yadda zai bunkasa ta hanyar da ta dace.

Haka kuma, tilas ne mu kara himma ba tare da kakkautawa ba, don ganin an sake hade Taiwan da babban yanki cikin lumana ba tare da kasala ba, da sa kaimi ga yin musanyar ra'ayi, da hadin kai da samun bunkasuwa, da nuna adawa da ballewa don samun 'yancin kai na Taiwan, da tsoma bakin kasashen waje, tare da hada kan 'yan uwanmu dake yankin Taiwan don yin aiki tare a kokarin farfado da kasa, da ma al'umma baki daya. (Ibrahim).