logo

HAUSA

Xi Jinping: Samun bunkasuwa mai inganci shi ne aiki na farko wajen gina kasa mai tsarin gurguzu ta zamani

2023-03-08 10:23:46 CMG Hausa

Yanzu haka ana gudanar da muhimman taruka biyu na kasar Sin, wato taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar (CPPCC) da na majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC). Inda ake fatan kammalawa a ranar 13 ga watan Fabrairun da muke ciki. A jawabinsa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yayin da yake halartar taron tattaunawa da tawagar wakilan lardin Jiangsu, a taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) karo na 14, ya jaddada cewa, samun bunkasuwa mai inganci shi ne aiki na farko kuma mafi girma wajen gina kasa mai tsarin gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni.

Xi ya ce, wajibi ne kasar Sin ta zurfafa yin gyare-gyare, da bude kofa, da sauya tsarin raya kasa, don hanzarta kafa cibiyoyi masu dorewa, da hanyoyin samun bunkasuwa mai inganci. Ya kara da cewa, kara kaimi wajen samun dogaro da kai, da karfin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha, ita ce hanyar da ya kamata kasar Sin ta bi wajen samun ci gaba mai inganci.

Ya jaddada cewa, kara karfin aikin noma, shi ne ginshikin babbar kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani, kuma inganta zamanantar da aikin gona, muhimmin abu ne wajen samun ci gaba mai inganci.

Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, farin ciki da jin dadin jama'a, shi ne babban burin sa kaimi ga samun ci gaba mai inganci. Yana mai cewa, matakin farko na tabbatar da shugabanci da jin dadin jama'a, na da matukar muhimmanci ga muradun jama'a, kuma suna da muhimmanci wajen ciyar da wadata da gina rayuwa mai inganci. Bugu da kari shugaban na kasar Sin Xi Jinping ya gana da mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, wadanda suka fito daga kungiyar dake rajin kafa kasa ta demokuradiyya ta kasar Sin da hadaddiyar kungiyar masana’antu da kasuwanci ta kasar jiya Litinin, inda ya kara karfafa wa kamfanoni masu zaman kansu gwiwa da su kara kokari domin cimma burin tabbatar da ingancin ci gaban tattalin arziki bangarori masu zaman kansu. Yawancin mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar da suka fito daga wadannan kungiyoyin biyu sun hada da masanan tattalin arziki da ‘yan kasuwa masu zaman kansu.

Xi ya kara da cewa, ya dace kamfanoni masu zaman kansu su kara fahimtar sabon tunanin raya tattalin arziki, ta yadda za su cimma burin tabbatar da ci gaba mai inganci. Kuma ya kara karfafa wa ‘yan kasuwan kasar gwiwar zuba jari kan manyan ayyukan kasa, domin sauke nauyin dake wuyansu na ingiza wadatar daukacin al’ummar Sinawa. (Fa’iza, Ibrahim /Sanusi Chen)