logo

HAUSA

A yau ne aka yi jana’izar Souley Abdoulaye tsohon faraministan Nijar

2023-03-08 09:16:59 CMG Hausa

A ranar Talata 7 ga watan Maris din shekarar 2023, shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum, ya halarci a fadar shugaban kasa ga bukukuwan jana’iza a hukumance na marigayi Souley  Abdoulaye, tsohon faraministan Nijar, da Allah ya wa rasuwa a ranar Laraba 1 ga watan Maris din shekarar 2023 a birnin Paris na kasar Faransa, bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Wakilin mu Mamane Ada, daga birnin Yamai ya aiko mana da wannan rahoto.

Tare da halartar mataimakin shugaban majalisar dokoki, Alkabous Jalaoui, da ke wakiltar shugaban majalisar dokoki, da faraminista Ouhoumoudou Mahamadou, da tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou, da kuma babban wakilin shugaban kasa Foumakoye Gado, haka kuma tare da kasancewar shugabannin hukumomin gwamnati, mambobin gwamnati, ’yan majalisar dokoki, jami’an diflomasiya, da sauran manyan mutane sojoji da fararen hula da ma iyalan mamacin wannan bikin jajantawa ya gudana.

Bayan shugaban kungiyar addinin musulunci ta Nijar ya gabatar da adu’o’i, shugaban kasa ya yi nasa juyayi da adu’o’i gaban gawar mamacin da ke lullube da tutar Nijar, sannan ya kuma gabatar da ta’aziyarsa ga iyalan mamacin.

An haifi miragayi Souley Abdoulaye, a 1965 a kauyen Kaoura Acha da ke cikin jihar Illela da ke yankin Tahoua, kuma ya rike mukamin ministan kasuwanci, da na sufuri da kuma na yawon bude ido da shakatawa, sannan ya rike kujerar ministan cikin gida kafin kuma ya rike kujerar faraminista. Souley Abdoulaye ya bar duniya a lokacin da yake da shekaru 58 a duniya.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.