logo

HAUSA

Sharhi: Burin Kasar Sin Na Samun Bunkasar GDP Da Kashi 5% A Bana Zai Cika

2023-03-08 20:03:45 CMG Hausa

Daga Abdulrazaq Yahuza

 

Masu zantukan hikima kan ce “da icce mai kama ake kota”, tabbas haka ne, domin duk lokacin da wata kasa ta tasa wani buri a gaba, a kan duba a ga ko abin nan da take son cimmawa mai yiwuwa ne ko zai zama tamkar gurguwa da auren nesa bisa la’akari da matakai da ta dauka da kuma waiwayen abubuwan da ta gudanar a baya.

A bana, kasar Sin ta kudiri aniyar bunkasa tattalin arzikinta da a kalla kashi 5% (cikin dari), kamar yadda firmanistan kasar, Li Keqiang ya sanar a cikin rahoton ayyukan gwamnati da ya gabatar a taron wakilan majalisar jama’ar kasar, ranar 5 ga watan Maris din nan, baya ga kuma za ta samar da sabbin ayyukan yi miliyan 12, daidaita zaman kashe wando a birane da kashi 5.5, karin kashi 3% a mizanin farashin masu amfani da kayan masarufi.

Wannan kudiri da kasar Sin ta tsara cimmawa mai yiwuwa ne saboda dama kasar ba ta kwanta sai da zakara. Da farko abin da za a yi la’akari da shi, shi ne yadda kasar ta rika samun matsakaicin bunkasar tattalin arziki da mizanin 5.2% a cikin shekaru 5 da suka wuce, da kuma iya cin jarrabawar da bullar cutar COVID-19 ta yi mata, sai kuma wasu matakai da a halin yanzu ta dauka don cimma burin nata na samun ci gaba da kashi 5%.

Duk da cewa a shekarar 2022, kasar ba ta iya cimma kason da ta yi hankoron cimmawa a farko-farkon 2022 ba saboda wasu dalilan da suka shafi annobar COVID-19 da koma-bayan tattalin arzikin duniya, amma ta yi kokari da ta samu ci gaba da kashi 3% domin ba abu ne mai sauki a iya samun hakan ba a yanayi mai wuyar sha’ani da kan fado waka’an (ba-zata).

Har ila yau, matakan da kasar ta dauka domin tayar da komada daga COVID-19 a karshen bara da yadda kasar ta nuna kwazo a hada-hadar sarrafa kaya da cinikinsu da kuma ci gaban da ta samu na GDP a sulusin karshe na 2022 da kashi 2.9, duk sun zarce hasashen da aka yi na samun bunkasa, don haka wannan manuniya ce ga yiwuwar cimma burin kasar na bunkasa GDP da kashi 5%.

Bugu da kari, tun a farkon wannan shekarar, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba sakamakon kyawawan tsare-tsare da manufofi da gwamnatin kasa da ta kananan hukumomi suka dauka ta bangaren kudi, zuba jari, inganta yanayin kasuwanci da amfani da kayan masarufi da sauransu.

Bayanan da Hukumar Kididdiga ta Sin ta fitar a ranar 1 ga Maris, sun nuna an samu ci gaban sayen kayan da kasar Sin ta sarrafa a watan Fabrairu fiye da na watan Janairu da kashi 2.5. Wannan ya kara gaskata bayanan da aka fitar kwanan baya game da yadda farfadowar tattalin arzikin Sin ke samun ci gaba.

Don haka ma, galibin cibiyoyin da ke auna bunkasar tattalin arziki na duniya sun yi yakini game da habakar tattalin arzikin kasar Sin a bana, inda suka rika daga ma’aunin mizanin da suke hasashe a kai a kai. Misali, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Sin zai bunkasa zuwa kashi 5.2% a bana. Haka nan mizanin Cibiyar Nomura Securities ya kyautata hasashen ci gaban zuwa kashi 5.3% daga kashi 4.8%. Ita ma Cibiyar Goldman Sachs ta yi hasashen abin zai  kai 5.5%, sai kuma Morgan Stanley da hasashenta ya dara na kowa a cikinsu da ta ce tattalin arzikin na Sin zai bunkasa ne da kashi 5.7%.

Sakamakon dunkulewar tattalin arzikin duniya, ba shakka, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai taimakawa ci gaban duniya.

Misali a Afirka, kasar Sin ta zama gagarabadau wajen bunkasa manyan ayyukan more rayuwa a kasashe daban-daban da suka hada da hanyoyi, sufurin jiragen kasa, madatsun ruwa, filayen jiragen sama, tashoshin teku da sauransu. Aikin da aka kammala na gina tashar teku mai zurfi na Lekki a jihar Legas da ke Nijeriya da ya kai kimanin Dala Biliyan 1.5, daya ne daga cikin ire-irensa masu dimbin yawa a Afirka. Don haka samun ci gaban tattalin arzikin Sin da kashi 5% zai ba ta dama ta samar da karin ayyukan ci gaba a Afirka.

Idan aka fadada zuwa duniya kuwa, ci gaban da kasar Sin za ta samu da kashi 5% zai taimaka wajen cike gibin da ake da shi a duniya, domin cinikayyar fitar da kaya da shigar da su a tsakanin Sin da kasashe za ta habaka. Kana ana sa rai Sin ta ba da gudunmawa ga bunkasar ci gaban duniya a 2023 da kashi 30 cikin 100.

Wannan tsari baro-baro a fili yake cewa babu tantama hakar kasar ta Sin za ta cimma ruwa bisa fafutikar da take yi wajen gina kasa ta zamani mai bin tsarin gurguzu a dukkan sassan rayuwa.