logo

HAUSA

Hukumomin Diffa sun sassauta matakan hana zirga-zirgar a daidaita domin kawo sauki ga mutane

2023-03-08 09:21:45 CMG Hausa

Shekaru 8 ke nan da kungiyar Boko Haram ta fara kai hare-harenta a yankin Diffa mai iyaka da Najeriya. A takaice a ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar 2015, kungiyar ta kai harinta na farko a karamar hukumar Bosso. Lamarin da ya janyo matsalar tsaro da tilastama gwamnatin Nijar ayyana dokar ta bace domin magance abkuwar hare-hare, matakin da duk da amfaninsa ya raunana tattalin arzikin yankin, musamman ma a bangaren noma, kiwo da kamun kifi.

Game da wannan batu, daga birnin Yamai, wakilinmu, Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Sannu a hankali ne, yankin Diffa ke samun farfadowa, tare da dawowar zaman lafiya da kuma dawowar hada-hadar tattalin arziki, inda tuni ma al’umomin yankin na Diffa suka fara nuna fatansu na ganin an janye wasu matakan tsaro domin saukaka zirga-zirga da shige de fice na mutane da dukiyoyinsu, musamman ma game da ababen sufuri kamar adaidaita. Dalilin hukumomin wurin da suka hada gwamnan Diffa, sarkunan gargajiya, da magajin garin birnin Diffa da sauran masu ruwa da tsaki, suka tattauna kan yadda za a dawo da zirga-zirgar adaidaita. Madam Asama’u Kanta, magajin garin Diffa ta yi karin haske game da matakan sassauta da saukaka zirga zirgar adaidaita.

Madam Asama’u Kanta:Mun tattauna kan yadda za a yi a maido wadannan ’yan adaidaita su yi aiki, an yi sharuda da yawa, a yanzu da farin mun dauki niyya mu samu a saki 40 da taxi 10, zaman da muka yi mun bayyana ma mutane abubuwan da muka tsaida, da matakan da muka dauka, sai mutane suka yi tsokaci, suke nuna rashin gamsuwarsu game da yawan adaidaita da aka saki, tun da akwai garuruwa da suke cikin daji, kuma an dubi girman garin Diffa, kuma mun dubi malaman makaranta da ma’aikata, masu tafiya da fita waje da cikin garin Diffa, sai na ce ni ba ni da ikon kayyade ko in rage, sai na yi ma magabatana shawara kan abin da muka yi, masha Allah, mun tattauna da gwamna, ya ce tun da haka nan ne ya zamanto duk dan adaidaita idan yana da adaidaita idan dan Nijar ne, in kuma wanda yake da adaidaita dan Nijar ne a sake su su yi zirga-zirgarsu cikin garin Diffa, amma dauke da sharuda da aka tsara. Amma yanzu an fara nuna bisa kan 40 da za a tantance ba tsayawa ba nan za a yi kuma, gobe wadansu 40 ne za a dauka har sai an samu a ida a samu adaidaita din har iyakacin inda za a same su sosai. Ke nan ba a kayyade ba a ce 40 ko 50, a’a iyakacin motuna na dan Nijar, amma kuma bincike idan aka fara binciken nan cigaba za a yi shi, ba a tsayawa.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.