logo

HAUSA

Xinjiang: An Inganta Kimanin Rabin Filayen Noma Zuwa Filayen Noma Masu Inganci

2023-03-08 20:40:17 CMG Hausa

Mahukuntan yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin sun bayyana, ya zuwa karshen shekarar 2022, yankin ya yi nasarar gina babban filin noma mai girman hekta miliyan 3.34, wanda ya kai kaso 47.39 na filayen noman yankin.

Sashen kula da harkokin noma da yankunan karkara na yankin ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, yankin Xinjiang ya ware kudin Sin RMB Yuan biliyan 2.07, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 297.88, don tallafawa aikin gina filayen noma masu inganci masu fadin hekta dubu 477. Wannan mataki ya taimaka wajen kara ingancin filayen noma matuka, tare da kara karfin noman hatsi da kashi 10 zuwa 20 cikin 100

Yankin zai kuma gina hekta dubu 277, da inganta hekta dubu 90 na filayen noma masu inganci, kana sannu a hankali ya mai da dukkan filayen noma na dindindin zuwa filayen noma masu inganci a shekarar 2023.

A cewar sashen kula da harkokin noma da yankunan karkara na yankin, a shekarar 2022, jimillar yawan hatsin da yankin na Xinjiang ya samar, ta karu tsawon shekaru 7 a jere. Kason hatsi na kowane mutum ya kai kilogram 700, karuwar kashi 44 cikin 100 kan na kasa baki daya.(Ibrahim)