logo

HAUSA

Najeriya ta bukaci mayakan ’yan a-waren kasar Chadi da su rungumi akidar hadin kan kasa

2023-03-07 09:21:54 CMG Hausa

A ranar 5 ga wata shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga ’yan a-waren kasar Chadi da su fifita bukatun hadin kan kasa maimakon kokarin rarraba kai ta hanyar fadace-fadace.

Shugaba Buhari ya bukaci hakan ne a Doha ta kasar Qatar yayin da yake karbar bakuncin shugaban gwamnatin rikon kwaryar Chadi Mahamat Idris Deby-Itno.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugabannin biyu wanda suke a kasar ta Qatar domin halartar babban taro karo na 5 na MDD kan kasashen da suke da karancin ci gaba na duniya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, babu abin da rashin zaman lafiya da rarrabuwa kawuna zai kawowa kasashen da suke kokarin tasowa ta fuskar ci gaba illa koma baya.

Ya ce hakika yana tausaya shugaban gwamnatin rikon kwaryar na kasar Chadi saboda ya gaji gwamanti da take da rauni ta fuskar tsaro da kuma ci gaban tattalin arziki.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, babban abin da gwamnatin kasar yanzu ke bukata shi ne samun haduwar kawuna na daukacin ’yan kasar domin dai tunkarar kalubale.

Ya kuma yi kira ga ’yan a-waren kasar da su shigo a dama da su wajen girka mulkin demokuradiyya a kasar ta Chadi.

A lokacin da yake yiwa manema labarai karin haske a game da tattaunawar shugabannin biyu, ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyema ya ce, shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin tallafin Najeriya wajen saita al’amura a kasar ta Chadi, duk da cewa ita ma Najeriya tana fuskantar irin nata kalubale.

Da yake nasa jawabin, shugaban gwamnatin rikon kwaryar  kasar ta Chadi Mahamat Idris Derby Itno godiya ya yi bisa irin taimakon da gwamnatin Najeriya ke baiwa kasar a shirye-shiryen da take yi na komawa kan tafarkin mulkin demokuradiyya.

Kamar dai yadda ministan harkokin kasashen ketare na Najeriya ya shaidawa manema labarai, ya ce jawabin na shugaban rikon kwaryar kasar ta Chadi ya mayar da hankali ne kan yadda ake samu ci gaba sosai ta fuskar samun fahimtar juna tsakanin gwamnati da kungiyoyin ’yan a-waren kasar.

“A kokarin daidaita al’amura a kasar ta Chadi yanzu haka daga cikin kungiyoyin siyasa na ’yan adawa guda 50 da ake da su a kasar, 40 daga cikinsu sun shiga cikin shirye-shiryen samar da sabuwar gwamnatin demokuradiyya a kasar ta Chadi, yayin da kuma ana nan ana ci gaba da tattaunawa da raguwar goman, kuma akwai kyakkyawan fatan su ma za su shigo cikin shirin. Daga karshen ya kara yabawa Najeriya saboda irin rawar da take takawa wajen taimakawa Chadi a kokarin ta na tabbatar da zama lafiya a kasar.”

A ranar Lahadin nan 5 ga wata aka fara babban taron  wanda za a kammala ranar Alhamis 9 ga wata, kuma kasashen 46 da suke da karancin ci gaba a duniya ne suke halartar taron. (Garba Abdullahi Bagwai)