logo

HAUSA

Labarin Wu Qunbin wanda ya taba koyar da yaren Sinanci a Najeriya

2023-03-07 15:38:40 CMG Hausa

Malam Wu Qunbin, dan kasar Sin ne wanda ya fara koyar da harshen Sinanci a kwalejin Canfucius ta jami’ar Nnamdi Azikiwe dake birnin Awka a jihar Anambra dake kudu maso gabashin Najeriya. An kafa kwalejin Confucius din a watan Maris na shekara ta 2008, bisa hadin-gwiwar jami’ar Xiamen ta kasar Sin da jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Najeriya.

Malam Wu ya ce, akasarin daliban dake koyon yaren Sinanci a makarantar sa, ba su da kudi sosai, wato iyayen su ba su iya ba su cikakken tallafin karatu. Amma hakan bai sanyaya gwiwar daliban wajen koyon yaren Sinanci ba, saboda a ganin su, harshen Sinanci zai bude musu sabon babi wajen rayuwa da aiki a nan gaba.

Wu ya ce, abun da ya burge shi shi ne, dalibai ‘yan Najeriya a kwalejin Confucius da yake aiki, suna matukar sha’awa, da himmatuwa sosai wajen karatun yaren Sin, ko a aji, ko kuma a ofis, ko’ina ana samun dalibai masu sha’awar karatun yaren Sin, al’amarin da ya kara karfafa gwiwar malam Wu wajen koyar da yaren.

Kwalliya ta biya kudin sabulu. Akwai dalibai ‘yan Najeriya da dama da suka iya magana da harshen Sinanci a cikin shekara daya ko biyu kawai, wasu ma har sun iya rubutu. Wani abu mai muhimmanci shi ne, ta hanyar koyon yaren Sin, rayuwar wasu dalibai ta canja, har ma sun cimma burikansu cikin nasara.

Duk wani dalibi ko wata daliba dake karatu a kwalejin Confucius na da wani suna a cikin yaren Sin. Dan Najeriya mai suna Wu Wenzhong a yaren Sin, ya fara koyon harshen Sinanci tun daga shekara ta 2010, daga bisani a watan Satumbar shekara ta 2013, ya samu kyautar tallafin karatu har ya tafi zurfafa karatun yaren Sin a jami’ar horas da malaman koyarwa ta Hebei dake arewacin kasar Sin, inda ya ci gaba da karatun digiri na farko da na biyu a fannin bada ilimi.

‘Yar Najeriya mai suna Xia Xiaoli a yaren Sin, tana fama da ciwon hannun dama, sakamakon wani hatsarin mota da ta gamu da shi lokacin da take da shekaru 5 da haihuwa, al’amarin da ya sa ba ta son mu’amala da jama’a sosai. A shekara ta 2015, Xia Xiaoli ta fara koyon yaren Sin a ajin kwalejin Confucius dake jami’ar Nnamdi Azikiwe, inda ta fara samun karfin gwiwa ta hanyar karatu. Duba da yadda take jin yaren Sin, ta samu aikin yi a wani kamfanin kasar Sin a wajen, har ma ta fara tallafawa ‘yan uwan ta maza da mata don su koyi yaren. Daga bisani a shekara ta 2017, Xia Xiaoli ta samu kyautar tallafin karatu da ya kai ta jami’ar Xiamen ta kasar Sin don ci gaba da karatun yaren Sin. Sa’annan a shekara ta 2018, ta kara samun kyautar tallafin karatu da ya kai ta jami’ar Hebei don karatun digiri na farko a fannin harkokin bada ilimi. Xia Xiaoli ta ce: “Harshen Sinanci ya karfafa mini gwiwa, ina godewa damar da kwalejin Confucius ta ba ni.”

Malam Wu Qunbin ya ci gaba da cewa, duk da cewa akwai nisan gaske tsakanin Najeriya da gida kasar Sin, kuma akwai kalubale a fannin aiki da rayuwa, amma shi da sauran malaman kasar Sin sun nuna himma da kwazo wajen koyar da yaren Sin, abun da ya kara karfafa zumunta tsakanin su da daliban Najeriya.

Tang Qiaohua, matar malam Wu Qunbin, ita ma malama ce dake koyar da yaren Sin a jami’ar Nnamdi Azikiwe. Wu ya ce, da su da daliban su tamkar ‘yan gida daya ne, kuma ‘yan Najeriya su kan kira su baba da mama daga kasar Sin.

A watan Oktoban shekara ta 2013, malam Wu da malama Tang suka gama aikin koyarwa a wani reshen dake kwalejin Confucius ta jami’ar Nnamdi Azikiwe. Kafin sun bar wajen, daliban su sun ba su kyautar wani zane, abun da ya sa malama Tang zub da hawaye sosai. Malam Wu ya ce, maimakon daukar hoton aure, sun rataya wannan zane a bangon dakin auren su, don kada su manta da irin dadadden zumunci da alakar ‘yan uwantaka tsakaninsu da dalibai ‘yan Najeriya.

A watan Fabrairun shekara ta 2018, malam Wu Qunbin, da malama Tang Qiaohua, gami da shugaban kwalejin Confucius ta jami’ar Nnamdi Azikiwe Wang Bo suka gama ayyukansu gaba daya suka dawo kasar Sin, inda daliban su daga Beijing, da Hebei, da Tianjin, suka tafi filin jirgin sama na Beijing don tarbarsu.

Malam Wu ya kara da cewa, yayin da yake aiki a Najeriya, shi da daliban sa sun dauki aniyar cewa, za su hadu a birnin Xiamen, idan suka samu damar karo ilimi a kasar Sin. A watan Fabrairun shekara ta 2019, daliban sa daga sassa daban-daban na kasar Sin, ciki har da Beijing, da Jilin, da Hebei, da Shandong, da Hubei suka taru a Xiamen, inda suka waiwayi karatun da suka yi a Najeriya, da kara kulla zumunta tsakanin su.

Wu Qunbin ya ce, ganin yadda dalibai suka samu ayyukan yi bisa harshen Sinanci, abu ne da ya faranta masa rai sosai, inda a cewar sa, ‘yan Najeriya dake jin yaren Sinanci na kara samun karbuwa a kasar su, kuma akwai daliban sa da yawa da suka samu ayyukan yi masu albashi mai tsoka.

Dan Najeriya mai suna Qi Xiaotian a yaren Sin, dalibi ne wanda ba shi da arziki sosai. A shekara ta 2012, ya raka wani abokin karatun sa yin rajistar koyon yaren Sin a kwalejin Confucius dake jami’ar Nnamdi Azikiwe, inda shi ma ya fara kaunar yaren Sin. A watan Satumban shekara ta 2013, ya samu kyautar tallafin karatu don koyon yaren Sin a jami’ar Xiamen na tsawon shekara guda. Da ya kammala karatu ya koma gida Najeriya a shekara ta 2014, ya samu wani aikin yi mai albashi mai kyau, abun da ya sa yanayin rayuwar ‘yan gidan sa ya kyautata kwarai da gaske.

A nata bangaren, dalibar kwalejin Confucius mai suna Liu Ying a yaren Sin, ta taba taimakawa kamfanonin kasar Sin da yawa yin rajista da gudanar da ayyuka a Najeriya, abun da ya kara kwarewar ta wajen aiki, da samun yabo daga abokan aikin ta, har ma wani kamfanin Sin ya ba ta mukamin aiki na mai taimakawa babban manajan su. A ganin Liu Ying, kara fahimtar yanayin da ake ciki a kasar Sin, ya sa ta kara sha’awar yin koyi da kasar don samar da ci gaba ga kasar ta Najeriya. 

Malam Wu Qunbin ya ce, taimakawa horas da kwararru a yaren Sinanci, babban buri ne da kwalejin Confucius dake jami’ar Nnamdi Azikiwe ke kokarin cimmawa har kullum. Alal misali, kwalejin sa ta kulla hadin-gwiwa da kamfanonin Sin da Najeriya da dama, don gabatar musu da dalibai ‘yan Najeriya masu jin yaren Sinanci da adadin su ya haura dubu 1, al’amarin da ba samar wa dalibai guraban ayyukan yi kawai ya yi ba, har ma ya taimaka sosai ga kamfanonin kasar Sin su kyautata ayyukan su a Najeriya, da bada gudummawa wajen inganta hadin-gwiwar kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da kasuwanci, da kara dankon zumunta a tsakanin su.

Malam Bahaushe kan ce, waiwaye adon tafiya. Malam Wu Qunbin ya ce, yana matukar alfahari da samun damar gudanar da aikin koyar da yaren Sinanci a Najeriya, da taimakawa ‘yan kasar cimma burikansu. Nan gaba kuma, zai ci gaba da yin kokarin don kara karfafa hadin-gwiwa da mu’amala da samun fahimtar juna tsakanin kasar Sin da kasashen ketare, musamman kasashen Afirka. (Murtala Zhang)