logo

HAUSA

Qin Gang ya yi tsokaci kan hulda tsakanin Sin da Amurka da hulda tsakanin Sin da Rasha

2023-03-07 13:12:08 CMG Hausa

A yau da safe ne babban taro karo na farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 ya kira taron ganawa da manema labarai, inda ministan harkokin wajen kasar Qin Gang ya amsa tambayoyin da manema labarai na Sin da waje suka yi masa game da manufar diplomasiyya ta kasar Sin da huldar dake tsakaninta da kasashen waje.

Game da huldar dake tsakanin Sin da Amurka, Qin Gang ya bayyana cewa, har yanzu Amurka na yiwa kasar Sin bahaguwar fahimta, inda ta mayar da kasar Sin a matsayin abokiyar gaba dake yin takara da ita, don haka tana aiwatar da manufar da ba ta dace ba kan kasar Sin. Kuma Qin Gang ya kara da cewa, batun Taiwan yana da muhimmanci matuka ga moriyar kasar Sin, tushe ne mafi muhimmanci ga huldar dake tsakanin ksashen biyu wato Sin da Amurka.

Ban da haka yayin da yake karin haske kan huldar dake tsakanin Sin da Rasha, minista Qin ya yi tsokaci cewa, an kafa huldar dake tsakanin sassan biyu ne bisa tushen rashin kulla kawance, da rashin nuna kiyayya da kuma rashin yin adawa ga bangare na uku, shi ya sa huldar dake tsakanin Sin da Rasha ba ta jawo kalubale ga sauran kasashen duniya baki daya ba. (Jamila)