logo

HAUSA

Jakadan kasar Sin a Niger ya gana da shugaban kasar

2023-03-07 10:23:43 CMG Hausa

Jakadan Sin a jamhuriyar Nijer, Jiang Feng ya gana da shugaban kasar Mohamed Bazoum a jiya, inda suka tattauna kan dangantakar kasashen biyu da hadin gwiwa kan wasu ayyuka na musamman.

A cewar jakada Jiang, taron wakilan JKS karo na 20, ya gabatar da shawarar inganta farfadowa da zamanantar da kasar Sin bisa nata salo. Kuma Sin za ta yi amfani da wannan dama wajen kara hadin gwiwa kan muhimman ayyuka da Nijer, tare da kai dangantakarsu zuwa sabon matsayi.

A nasa bangare, shugaba Bazoum ya ce Niger da kasar Sin muhimman abokan hulda ne, kuma a shirye Nijer din take ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da Sin da kara kyautata dangantakar dake tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)