logo

HAUSA

Xi: Ya dace a tabbatar da ingancin ci gaban tattalin arziki bangarori masu zaman kansu

2023-03-07 09:49:50 CMG Hausa

Shugaban kolin kasar Sin Xi Jinping ya gana da mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, wadanda suka fito daga kungiyar dake rajin kafa kasa ta demokuradiyya ta kasar Sin da hadaddiyar kungiyar masana’antu da kasuwanci ta kasar jiya Litinin, inda ya kara karfafa wa kamfanoni masu zaman kansu gwiwa da su kara kokari domin cimma burin tabbatar da ingancin ci gaban tattalin arziki bangarori masu zaman kansu. Yawancin mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar da suka fito daga wadannan kungiyoyin biyu sun hada masanan tattalin arziki da ‘yan kasuwa masu zaman kansu.

Yayin ganawar ta su, shugaba Xi ya sake jaddada cewa, kasar Sin tana nacewa kan manufar raya tattalin arziki mallakar gwamnatin kasa, tare kuma da raya tattalin arzikin bangarori masu zaman kansu.

Xi ya kara da cewa, ya dace kamfanoni masu zaman kansu su kara fahimtar sabon tunanin raya tattalin arziki, ta yadda za su cimma burin tabbatar da ci gaba mai inganci. Kuma ya kara karfafa wa ‘yan kasuwan kasar gwiwar zuba jari kan manyan ayyukan kasa, domin sauke nauyin dake wuyansu na ingiza wadatar daukacin al’ummar Sinawa. (Jamila)