logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya gana da manema labarai dangane da manufofin Sin kan kasashen waje

2023-03-07 11:13:14 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya kira wani taron manema labarai a yau Talata, a gefen zama na farko na taron majalisar wakilan jama’ar kasar karo na 14, inda ya amsa tambayoyin manema labarai na ciki da wajen kasar, dangane da manufofi da dangantakar Sin da kasashen waje.

A cewar Qin Gang, yayin da aka samu saukin annobar COVID-19 a cikin gida, kasar Sin tana dawo da huldar musaya tsakaninta da kasashen waje, kuma harkokinta na diflomasiyya sun samu karin kuzari, kuma tuni suka aike da sako mai karfi.

Ya kara da cewa, zamanantar da kasar Sin mai yawan al’umma sama da biliyan 1.4, abu ne da ba a taba gani ba a tarihin dan adam, wanda kuma ke da gagagrumar fa’ida ga duniya. Yana mai cewa, manufar zamanatarwar ta dace da yanayin da kasar ke ciki a zahiri.

Bugu da kari, ministan ya ce zamanantar da kasar Sin za ta bunkasa zaman lafiya a duniya da tabbatar da adalci da kuma ci gaba. (Fa’iza Mustapha)