logo

HAUSA

Xi ya jaddada samun ci gaba mai inganci a kokarin zamanantar da kasar Sin

2023-03-06 10:22:24 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada cewa, samun bunkasuwa mai inganci shi ne aiki na farko kuma mafi girma wajen gina kasa mai tsarin gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni.

Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban rundunar sojojin kasar, ya bayyana hakan ne jiya Lahadi, yayin da yake halartar taron tattaunawa da tawagar wakilan lardin Jiangsu, a taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) karo na 14, wato majalisar kafa dokokin kasar.

Xi ya ce, wajibi ne kasar ta zurfafa yin gyare-gyare, da bude kofa, da sauya tsarin raya kasa, don hanzarta kafa cibiyoyi masu dorewa, da hanyoyin samun bunkasuwa mai inganci.

Ya kara da cewa, kara kaimi wajen samun dogaro da kai, da karfin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha, ita ce hanyar da ya kamata kasar Sin ta bi wajen samun ci gaba mai inganci.

Xi ya jaddada cewa, kara karfin aikin noma, shi ne ginshikin babbar kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani, kuma inganta zamanantar da aikin gona, muhimmin abu ne wajen samun ci gaba mai inganci.

Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, farin ciki da jin dadin jama'a, shi ne babban burin sa kaimi ga samun ci gaba mai inganci. Yana mai cewa, matakin farko na tabbatar da shugabanci da jin dadin jama'a, na da matukar muhimmanci ga muradun jama'a, kuma suna da muhimmanci wajen ciyar da wadata da gina rayuwa mai inganci. (Ibrahim Yaya)