Amurka Ba Ta Kula Sosai Da Panda Da Ta Ara Daga Kasar Sin
2023-03-06 14:52:19 CMG HAUSA
DAGA MINA
Abokai, Panda wata dabba ce dake da tarihi na a kalla shekaru miliyan 8 a duniya, kuma dabba ce dake fuskantar barazanar bacewa baki daya daga doron kasa, hakan ya sa aka sanya sunanta cikin dabbar da dole a kiyaye ta. Yanzu Panda tana rayuwa ne a dajin kasar Sin kawai. Saboda yadda al’ummar sauran kasashe ke matukar son Panda, gwamnatin Sin ta fara bayar da aron Panda zuwa kasashe da suka cancanci ba da kulawa ga Panda, shi ya sa Panda ta zama dabba dake alamanta zumunci.
Amma, halin da Panda da Amurka ta ara dake gidan kula da dabobbi na Memphis ke ciki ba shi da kyau, abin da ya fusata mutane sosai. A watan Disamba na bara, wannan gidan dabobbi ya sanar da maido da Panda biyu ga kasar Sin saboda wa’adin shekaru 20 na kwangilar aron ta kare. Amma abin bakin ciki shi ne, wata Panda mai suna “LE LE” ta mutu sakamakon ciwon zuciya a watan da ya gabata. Dayar mai suna “Ya Ya” ita ma ba ta cikin hali mai kyau, idan Panda tana da lafiya, za a ga tana da kiba kamar siffar kwallo. Amma, “Ya Ya” yanzu tana fama da ciwon fata har gashin jikinta ya zube, rashin abinci mai inganci, ya sa ta rame.
A karnin da ya gabata, wasu ‘yan Amurka sun saci Panda daga Sin saboda ba su taba ganin irin wannan dabba ba. A shekarar 1936, wata mai attajira mai suna Rose ta kama wata Panda ta jigilar ta zuwa Amurka, daga waccan lokaci, ‘yan Amurka da Turai sun fara satar Panda daga Sin, amma, Panda ba za su iya rayuwa a wani wuri illa kasar Sin, saboda muhallin da Sin ke da shi kawai ya dace da rayuwar dabbar ta Panda, yawancinsu sun mutu a kan hanyar jigilarsu zuwa ketare, a wani lokaci ma dabbar ta kusa karewa daga doron kasa. Bayan kafuwar jamhuriyyar jama’ar kasar Sin, gwamnati a waccan lokaci ta hana irin wannan abu na rashin imani tare da fara kiyaye dabbar Panda.
Tabbatar da lafiyar jikin Panda wani muhimmin abu ne dake cikin kwangilar aro Panda da sauran kasashe za su kulla da Sin. Ban da wannan kuma, dokar tabbatar da hakkin dabobbi da Amurka ta zartas da ita a shekarar 1980, ta tanadi cewa, ya kamata a tabbatar da hakkin dabobbi, ciki hadda ba su kulawa yadda ya kamata da hana cin zarafinsu. Amma, Panda a matsayinta na dabbar dake alamanta zumunci, ba a kula da ita sosai ba a gidan dabobbi na Memphis na Amurka, abin da ya fusata duk wani mai son Panda, dabbar dake fuskantar barazanar karewa a doron kasa. Ba shakka, Amurka ba ta iya tabbatar da kare hakkin dabobbi ba, balle hakkin Bil Adama.
An hanzarta maido da “Ya Ya” gida nan kasar Sin, ta yadda za a ba ta kulawar da ta dace, don ganin ta warke da zaman rayuwa mai dadi. (Mai zana da rubuta: MINA)