Chen Jinning: Kasar Sin da nake so gida na ne
2023-03-06 23:05:40 CMG Hausa
Mene ne "gida"? Ga Sinawa, gida wuri ne na zama wanda ake iya samun kwanciyar hankali a ciki. Yanzu, dalibai da yawa na kasa da kasa dake karatu a nan kasar Sin suna jin dadi kan bambance-bambancen dake kasancewa da kuma saukin da ake samu a fannonin zaman rayuwa da karatu, wanda ci gaban al'ummar kasar Sin ke kawowa, sun kuma fahimci ra’ayin karbar baki da Sinawa ke bi tun cancancan da, wato "abin farin ciki ne idan an karbi abokai daga nesa", suna iya kwantar da hankulansu da jin yadda gida yake a nan kasar ta Sin. Chen Jinning da ta fito daga kasar Cambodia ita ma daya ce daga cikinsu.
Chen Jinning daliba ce ta jami'ar koyon ilmin kabilu ta Guangxi, akwai wani wurin shakatawa dake kusa da makarantarsu, Chen Jinning da abokanta su kan je nan don shakatawa. Yanzu tana tafiya tana kuma magana kan yadda ta zo kasar Sin.
“A yayin da nake da shekaru 10 da haihuwa, na zo nan kasar Sin karo na farko tare da iyaye na. A wancan lokacin, an gaya min cewa, idan na iya samun damar yin karatu a kasar a nan gaba, ko shakka babu zan zo, gaskiya ina so in zo. Yana da kyau a yi karatu a kasar Sin, yanayin makaranta yana da kyau sosai, kuma ana iya yin karatu tare da dalibai daga kasashe daban daban.”
Chen Jinning, wadda take son kasar Sin tun da ta zo kasar a karo na farko, yanzu dai tana aiki tukuru don koyon Sinanci.
Ita da kawayenta sun gaya mana cewa, a kasar Cambodia, akwai matasa da dama da ke koyon Sinanci, ba wai kawai suna kallon fina-finan kasar Sin ba, har ma suna son sauraron kide-kiden Sinawa, da kuma amfani da manhajojin sada zumunta na kasar. Ga wadannan matasa, Sinanci wata kofa ce a gare su don neman aikin yi da kuma kara yawan kudin shiga.
“A kasar Cambodia, mutane da yawa suna koyon Sinanci, kuma idan suna jin Sinanci, za su iya samun ayyuka masu kyau. Domin yanzu akwai Sinawa da yawa dake bude kamfanoni a kasar ta Cambodia.”
Kafin ta zo kasar Sin, Chen Jinning ta damu matuka cewa Sinancin ta ba shi da kyau, don haka zai yi wuya ta yi magana da wasu, ban da wannan kuma, ita yarinya 'yar shekara 20 ta je kasar waje don yin karatu ita kadai, don haka ta damu sosai kan ko za ta iya samun tsaro a kasar. Amma, bayan ta zo kasar Sin, ta gano cewa, wadancan abubuwan da ta damu ba su da amfani, ta ji cikakken tsaro a birnin Nanning dake da nisan kilomita fiye da 2,000 daga gidanta. Chen Jinning ta ce,
“Saboda ban iya Sinanci sosai ba, na ji tsoron ba zan iya yin hira da Sinawa ba, amma akwai mutane da yawa da ke hira da ni, sun ce na iya Sinananci, suna son yin hira da ni. Na kuma taba jin tsoron fita waje ni kadai, amma yanzu na gano cewa, ko da na fita waje ni kadai a Sin, to babu matsala ko kadan.”
Chen Jinning ta ce, abu mafi muhimmanci game da zama a kasar Sin shi ne ba a bukatar daukar tsabar kudi idan za fita waje. Ita da abokanta dukkansu suna matukar son ingantaccen tsarin biyan kudi ta wayar salula da kasar ke da shi.
“A nan kasar Sin, ba ma bukatar yawo da tsabar kudi da yawa, sai dai kashe kudi ta wayar salula. A kasar Cambodia, muna amfani da tsabar kudi a mafi yawan lokuta, ko da yake yanzu mu ma muna iya biyan kudi da wayar salula, amma ba a dade da fara amfani da wannan hanyar ba.”
A cikin wannan sabuwar shekara, Chen Jinning ta kafa wa kanta wata karamar buri, wato kara matsayin Sinancinta, samun karin abokai na kasar Sin, sa'an nan kuma kai ziyara Beijing, babban birnin kasar.
“Ina son inganta Sinanci na da kara samun abokai Sinawa. Ina son kara fahimta da koyon al'adun kasar Sin. Ina kuma so in je birnin Beijing don ganin filin Tiananmen da babbar ganuwa ta Great Wall.”
A cikin shekara fiye da daya da ta zauna a birnin Nanning, Chen Jinning ba kawai tana jin dadi, da samun kwanciyar hankali ba, har ma ta sami wasu abubuwan dake da alaka da garinsu a nan, kamar su irin yanayi da abinci, muhalli mai annashuwa, masu gadin da ke kula da su sosai, da dai sauransu. Tana zama a nan kamar yadda take a gida.
“Yanayin Nanning yana da kyau sosai, akwai bishiyoyi da wuraren shakatawa da yawa a nan, kuma muhalli yana da kyau sosai. Har ila yau, ina son abincin kwarai, musamman na Nanning. Ina tsammanin abincin Nanning sun yi kama da na Cambodia, hakan ya ya sa nake jin kamar ina gida.”
Da aka tambaye ta game da shirinta bayan kammala karatunta, Chen Jinning ta ce bayan ta koma garinsu, za ta yi amfani da ilimin da ta koya a kasar Sin don gina garinsu. Har ila yau, tana fatan karin daliban kasar Cambodia kamar yadda take, za su samu damar yin karatu a kasar Sin, don taka rawa wajen karfafa dangantakar dake tsakanin Cambodia da Sin.
“Bayan kammala karatuna, ina so in koma Cambodia, domin ina son in kai da ilimin da na koya a kasar Sin zuwa kasar Cambodia don taimakawa kasarmu wajen samun ci gaba. Na san cewa, kasar Sin ta shiga wani mataki na samun ci gaba mai inganci, kuma tattalin arzikin kasar Sin na bunkasuwa yadda ya kamata. Ina kuma fatan karin daliban Cambodia kamar ni za su sami damar yin karatu a kasar ta Sin. Ina fatan bunkasuwar kasar Sin za ta kara dorewa da inganci.”