logo

HAUSA

Gwamnatin Syria ta yi Allah-wadai da ziyarar da janar din Amurka ya kai yankin arewa maso gabashin kasar

2023-03-06 11:41:32 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria, ta yi Allah-wadai da ziyarar da wani babban hafsan sojan Amurka ya kai wani sansanin sojojin Amurka dake yankin arewa maso gabashin kasar.

A cikin wata sanarwar da ta fitar, ma'aikatar ta caccaki babban hafsan hafsoshin sojojin Amurka Janar Mark Milley, kan ziyarar ba zata da ya kai sansanin, domin ganawa da sojojin Amurka dake yankin arewa maso gabashin Syria.

Sanarwar ta ce, ziyarar tamkar cin zarafi ne ga ikon mulki da cikakkun yankunanta da kuma hadin kan kasar.

Bugu da kari, ma'aikatar ta bukaci gwamnatin Amurka da ta gaggauta dakatar da keta dokokin kasa da kasa, da ma goyon bayan da take baiwa mayakan ’yan aware masu dauke da makamai. (Ibrahim Yaya)