logo

HAUSA

Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasa Tattalin Arzikin Duniya

2023-03-06 20:57:31 CMG Hausa

An bayyana kasar Sin a matsayin wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya.

Irina Kokushkina, karamar farfesa a sashen nazarin tattalin arzikin duniya na jami’ar St. Petersburg ce ta bayyana haka, yayin zantawarta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan.

A cewarta, duk da kalubalen da aka fuskanta a bara, kamar na annobar COVID-19 da koma-bayan tattalin arzikin duniya, kasar Sin ta yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikinta.

Ta kuma zayyano wasu dalilai da suka haifar da ci gaban tattalin arzikin Sin a shekarar 2022, wadanda suka hada da tantance kalubalen da za a iya fuskanta tare da daukar matakan shawo kansu yadda ya kamata, da hada manufofin tafiyar da tattalin arziki da ka’idojin kasuwa ta yadda za su bunkasa tattalin arzikin kasar, da kuma dogaro da albarkatunta na cikin gida da karfin tattalin arzikinta. (Fa’iza)